Online counter

Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotun

Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotun

A jiya, Lahadi, ne shugaba Buhari ya bar  najeriya domin halartar wani taro a birnin Hague na kasar Holland inda zai gabatar da jawabi, kamar yadda kakakinsa, Garba Shehu, ya sanar tun ranar Asabar.
A wasu hotuna da shafin fadar shugaban kasa ta saki a shafinta dake Tuwita, an ga shugaba Buhari na gabatar da jawabi a wurin taron. Bayan kamala jawabinsa ne sai dukkan turawan da suka halarci taron suka dauki tafi, wata alama dake nuni da cewar jawabin na Buhari ya birge su.
Wani dan Najeriya mazaunin kasar Holland, Toyin Loyo, ya mika kyautar wani zanen Buhari da ya yi ga shugaban Buharin.
A zanen da ya yi, Loyo, ya rubuta cewar cewar shugaba Buhari tamkar wani haske ne da zai dusashe ba.
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Toyin Loyo da zanen Buhari
Bayan ya gabatar da jawabin, shugaba Buhari ya gana da wakilan kamfanin Heineken da Shell, da dukkansu keda reshe a Najeriya. Kazalika, shugaba Buhari ya gana da wasu ‘yan Najeriya dake zaune a kasar ta Holland. Duba hotuna;
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Ana tafawa shugaba bayan ya kammala jawabi
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Shugaba Buhari na gabatar da jawabi
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Shugaba Buhari da wakilan wasu kamfanoni
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Shugaba Buhari da wasu 'yan Najeriya dake kasar Holland
Shugaba Buhari na cigaba da burgewa a taron da yake halarta a kasar Holland, kalli hotuna
Shugaba Buhari da wasu 'yan Najeriya mazauna kasar Holland

Post a Comment

0 Comments