Online counter

Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar

Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar

Tsohon gwamnan jihar Imo a karkashin PDP, Ikedi Ohakim, ya bayyana ficewar sa daga jam’iyya tare da komawa jam’iyyar APGA inda yake saka ran zai yi takarar gwamna a cikinta a zaben shekarar 2019.
Ohakin ya sanar da ficewarsa daga PDP ne a jiya juma’a yayin da yake jawabi ga dandazon magoya bayan jam’iyyar APGA a filin wasa na Kanu Nwankwo dake Owerri, babban birnin jihar ta Imo.
Ya ce zai yi amfani da gogewarsa a matsayin tsohon gwamna domin kawowa jihar Imo cigaban da take bukata da kuma kubutar da ita daga mulkin kama karya irin na jam’iyyar APC, kamar yadda ya fada.
Neman mafaka: Tsohon gwamnan PDP ya fice daga jam’iyyar
Ikedi Ohakim
Tsohon gwamnan ya kara da cewa a yanzu haka jam’iyyar APGA ce kadai keda mutuncin da zai iya shiga domin yin takarar neman 
Daga karshe ya bukaci duk ‘yan asalin jihar ta Imo dake gida Najeriya da ketare das u bashi hadin kai domin ya samu dammar cimma burinsa na kara mulkar jihar a karo na biyu tare da yi masu alkawarin zai mika mulki ga mutum mai mutunci day a fito daga Sanatoriyar Owerri da zarar ya kamala zangonsa daya na mulki.

Post a Comment

0 Comments