Online counter

Me ya kai fura zani?: Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP

Me ya kai fura zani?: Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP


- jaridar New Telegraph ta wallafa a yau, Litinin ya bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP
- An gudanar da taron gangamin ne a yau a dakin karatu da Obasanjo ya gina a garin na Abeokuta.
- Jam’iyyar PDP ta shirya taron ne domin gabatar da daya daga cikin ‘yan takararta na gwamna, Honarabul Adebutu, ga jama’a
Wani labari da jaridar New Telegraph ta wallafa a yau, Litinin ya bayyana cewar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP da aka yi a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Me ya kai fura zani?: Obasanjo ya halarci taron gangamin jam’iyyar PDP
Obasanjo
An gudanar da taron gangamin ne a yau a dakin karatu da Obasanjo ya gina a garin na Abeokuta.
Labarin na New Telegraph ya bayyana cewar Obasanjo ya halarci taron tare da yiwa jama’ar da suka hakarci wurin taron maraba.
Jam’iyyar PDP ta shirya taron ne domin gabatar da daya daga cikin ‘yan takararta na gwamna, Honarabul Adebutu, ga jama’a.
Saidai jaridar New Telegraph bata bayar da Karin bayani a kan bayyanar Obasanjo a wurin taron ba.

Post a Comment

0 Comments