Online counter

Kungiyar kwadago ta kasa ta rufe Ofishin MTN na jihar Kano

Kungiyar kwadago ta kasa ta rufe Ofishin MTN na jihar Kano

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Kano ta bi sahun sauran takwarorinta na jihohi wajen rufe ofishin kamfanin sadarwa na MTN da ke fadin jihar nan ta hanyar gudanar da zanga-zanga a wani yunkuri na daukan mataki kan yadda kamfanin ke bautar da ma’aikatansa.
Kungiyar ta NLC dai ta mamaye bakin ofishin na MTN tun da misalin karfe 6 : 30 na safiyar yau, Litinin, inda suka hana ma’akata shiga ofishin tare da dakatar da gudanar da al’amura a daukacin kamfanunwan da ke nan Kano.
Kungiyar kwadago na yiwa MTN zanga-zanga ne bisa yadda suke bautar da ma’aikatansu duk da kasancewar suna daukansu ne a matsayin ma’aikata na wucin gadi.
Kungiyar kwadago ta kasa ta rufe Ofishin MTN na jihar Kano
Masu zanga-zanga a Ofishin MTN na jihar Kano
Da yake jawabi yayin zanga-zangar, shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kano, Kabiru Ado Minjibir, ya yi ga gwamnati da ta shiga cikin lamarin kamfanin na MTN domin nemawa jama’a hakkinsu.
Minjibir ya kara da cewa, “kamar yadda uwar kungiyar NLC ta kasa ta umarce mu, ba zamu bar harabar kamfanin MTN ba sai shugabanninsu sun fito sun yi mana jawabi a kan zarge-zarge da ake yiwa kamfaninsu.”
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar masu zangar-zangar sun mamaye kofar shiga kamfani MTN inda suka yi dafifi suna rawa da waka.
Saidai har zuwa lokacin da muka kamala hada wannan rahoto babu wani daga cikin jami’an kamfanin na MTN day a fito domin yin jawabi ga masu zanga-zangar.

Post a Comment

0 Comments