Online counter

Kotu ta umarci wasu manyan sojoji mayar da miliyan N200m da suka wawure

Kotu ta umarci wasu manyan sojoji mayar da miliyan N200m da suka wawure

- Wata kotun gwamnatin tarayya dake Legas ta umarci wasu manyan sojoji biyu su mayar da miliyan N200m da suka wawura
- Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annaci (EFCC) ce ta gurfanar da tsofin sojojin da wasu kamfanoni da suka yi amfani da su wajen wawurar kudaden
- Alkalin kotun, Muslim Sule Hassan, ya umarci sojojin su mika miliyan N200m ga EFCC na wucin gadi
Wata kotun gwamnatin tarayya dake Legas ta umarci wasu manyan sojoji biyu su mayar da miliyan N200m da suka wawura tare da boyewa a wasu bankunan kasar nan.
Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta'annaci (EFCC) ce ta gurfanar da tsofin sojojin da wasu kamfanoni da suka yi amfani da su wajen wawurar kudaden.
Kotu ta umarci wasu manyan sojoji mayar da miliyan N200m da suka wawure
Kotu ta umarci wasu manyan sojoji mayar da miliyan N200m da suka wawure
EFCC ta shaidawa kotu cewar wadanda ake tuhuma sun fitar da kudaden ne daga asusun hukumar tsaro ta hanyar amfani da wasu uzuri na bogi.
Sojojin biyu, Adamu Bello Argungu da John Onimisi Ozigi, an gurfanar da su tare da kamfanin Falsal & Co Global da Diamond Head Ventures & Development Company Limited da kuma Sweetex Bureau De Change Limited.
Alkalin kotun, Muslim Sule Hassan, ya umarci sojojin su mika miliyan N200m ga EFCC na wucin gadi bayan ya kammala sauraron lauyan hukumar ta EFCC, Nkereuwem Mark Anana. Lauyan na EFCC ne ya roki kotun ta kwace kudaden na wucin gadi zuwa lokacin da za a kammala shari'ar.

Post a Comment

0 Comments