Online counter

Jama'a a lura: Hukumar 'yan sanda ta ankarar da 'yan Najeriya wasu sabbin dabaru da masu satar mutane suka bullo da su

Jama'a a lura: Hukumar 'yan sanda ta ankarar da 'yan Najeriya wasu sabbin dabaru da masu satar mutane suka bullo da su

A wata sanarwa da jami'in dan sanda, Abba Kyari, ya fitar, hukumar 'yan sanda ta ankarar da 'yan Najeriya wasu sabbin dabaru da masu garkuwa da mutane da 'yan fashi suka bullo da su na boye bindiga da makamai a cikin injin mota.
A ranar 9 ga watan Yuli ne sashen hukumar 'yan sanda na IRT (intelligence response team) ya kama wasu 'yan fashi da makami 6 da suka addabi wasu jihohin arewa ta tsakiya.
An kama 'yan fashin ne a jihar Kwara kuma an yi nasarar gano bindigu 4 da alburusai fiye da 500 boye cikin injin motar su kirar Mazda, kamar yadda zaku iya gani cikin faifan bidiyon dake kasa.

'Yan ta'addar su ne:
Yayin da suke amsa tambayoyin jami'an 'yan sanda, 'yan ta'addar sun bayyana yadda suka aikata fashi da satar mutane a Kogi, Kwara, Abuja da Kaduna.
1. Nelson Yakubu mai shekaru 36, dan asalin karamar hukumar Dakina ta jihar Kogi, wanda kuma shine shugaban 'yan ta'addar.
Jama'a a lura: Hukumar 'yan sanda ta ankarar da 'yan Najeriya wasu sabbin dabaru da masu satar mutane suka bullo da su
'Yan ta'adda da aka kama
2. James Obaje mai shekaru 34, dan asalin karamar hukumar Dakina ta jihar Kogi.
3. Yakubu Danladi, mai shekaru 27, dan asalin karamar hukumar Ankpa ta jihar 
4. Ibrahim Mutari; mai shekaru 25, dan asalin karamar hukumar Dakina ta jihar Kogi.
5. Suleiman Ilo; mai shekaru 35, dan asalin karamar hukumar Omala ta jihar Kogi.
6. Gboyega Olaoye; mai shekaru 35, Dan asalin karamar hukumar Ekiti dake jihar Kwara.

Post a Comment

0 Comments