Online counter

Ganin an fara yi mata dauki dai-dai, APC ta nemi ƴan rAPC damar sulhu

Ganin an fara yi mata dauki dai-dai, APC ta nemi ƴan rAPC damar sulhu

- Sakamakon karatowar zaben 2019 da kuma yadda wasu 'yan jam'iyyar APC suka fara kaura yanzu haka an fara neman su zo ai sulhu
- rAPC ce dai ta fara yin gaba kuma ana raderadin sake ficewar wasu zuwa jam'iyyar PDP
- Babban abinda yake gaban sabon shugaban jam'iyyar APC shi ne shawo kan masu shirin ficewa daga jam'iyyar
Jamiyyar APC ta shawarci fusatattun magoya bayanta akan su yi amfani da damar yin sulhu da shugabancin Jamiyyar ya tanadar. Jamiyyar APC ta shawarci fusatattun magoya bayanta akan su yi amfani da damar yin sulhu da shugabancin Jamiyyar ya tanadar.
Ganin an fara yi mata dauki dai-dai, APC ta nemi ƴan rAPC damar sulhu
Ganin an fara yi mata dauki dai-dai, APC ta nemi ƴan rAPC damar sulhu
Jamiyyar ta yi wannan kiran ne cikin wata sanarwa da kakakin jami'yyar na kasa Malam Bolaji Abdullahi ya sanyawa hannu a ranar Talatan nan. Sanarwar ta kara da cewa shugabancin jami'yyar ya himmatu wajen hakurkurtar da fusatattun yayanta.
Sanarwar na a matsayin mayar da martani akan yarjejeniyar da jami'yyar PDP ta kulla a tsakaninta da sauran jam'iyyu a jiya.
Tun da farko dai fusatattun yan jamiyyar APC din sun ware kansu daga cikin jami'yyar inda su ka kafa sabuwar Jami'yyar APC mai taken rAPC karkashin jagorancin tsohon sakataren rushashshiyar Jami'yyar CPC na kasa wato Engr. Buba Galadima.
Hadakar jamiyyun dai sun hadar da Jami'yyar PDP da SDP da kuma sauran jamiyyu, wanda za su kalubalanci shugaban kasa Muhammad Buhari a kakar zaben shekarar 2019.
Mal. Bolaji Abdullahi ya ce wannan hadakar ba za ta hana yakin da shugaba Muhammad Buhari ya ke akan cin hanci da rashawa ba. Sannan ya kara da cewa Jami'yyar tana bayar da cikakken goyon baya wajen inganta rayuwar al'ummar kasar nan.
"Jamiyyar APC tana girmama ra'ayoyin al'ummar kasar nan, sannan kuma tana nan a dunkule, domin tsagin rAPC ba tsagi ba ne daga Jamiyyar APC" in ji Bolaji Abdullahi
A karshe sanarwar ta bayyana cewa da yawa daga cikin jamiyyu sun nesanta kansu daga hadakar da Jamiyyar PDP suka shiga da sauran jam'iyyu.

Post a Comment

0 Comments