Online counter

Dalilin da ya saka shugabannin R-APC shiga PDP cikin gaggawa

Dalilin da ya saka shugabannin R-APC shiga PDP cikin gaggawa

A jiya ne, Mista Babatunde Ogala, mai bawa APC shawara a kan harkokin shari’a ya zayyana wasu laigukan ta’addanci hudu (4) da shugabannin tsagin R-APC suka yiwa jam’iyyarsu tare da bayyana cewar zasu maka su a kotu domin koya masu hankali da kuma koyawa masu sha’awar irin halinsu darasi.
Ogala ya bayyana cewar, taka doka ne da kuma rashin ilimin shari’a ya saka shugabannin R-APC ayyana kungiyarsu a matsayin jam’iyya ba tare da bin tsarin da doka ta tana ba ga duk wata kungiya dake burin zama jam’iyyar siyasa.
Sannan ya kara da cewa, shugabannin R-APC sun yiwa jam’iyyar APC satar fasaha ta hanyar amafani da harufan APC a cikin kungiyarsu. Wanda yin hakan shi ma laifi ne mai zaman kansa da yake da hukunci ca a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Dalilin da ya saka shugabannin R-APC shiga PDP cikin gaggawa
Shugabannin R-APC yayin hada gwuiwa daa PDP
Ogala bai tsaya haka ba, saida ya kara da cewar, R-APC sun yiwa shugabannin jam’iyyar APC sojan gona ta hanyar bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar APC na hakika. Sannan ya kara da cewa, yin hakan laifi ne babba da jam’iyyar APC ba zata kyale ba.
Wani laifi da Ogala ya kara zargin shugabannin R-APC da aikatawa shine na nuna raini ga hukumar zabe ta kasa (INEC) ta hanyar nuna cewar zaben shugabannin jam’iyyar APC haramtacce ne bayan INEC din ta halasta zaben.
Ganin cewar basu da ragowar wani uzuri ko hujja da zasu yi amfani da ita wajen kare kansu domin cigaba da zama a jam’iyyar APC, shine suka ga gara su fice daga jam’iyyar dungurungum su huta, kamar yadda masu fashin bakin siyasa suka bayyana.
Abun jira a gani shine ko APC zata shigar da kararsu bisa laifukan da ta zayyana duk da kasancewar yanzu basa cikin jam’iyyar.

Post a Comment

0 Comments