Online counter

Da duminsa: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa

Da duminsa: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa

Shugaba Buhari ya bukaci magoya bayansa da su sassauta da yi masa yakin neman zaben shekarar 2019 domin yin hakan sabawa dokar hukmar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ne.
A jawabin da mai ba shi shawara a bangaren yada labarai, Femi Adesina, ya fitar a yau, Asabar, Buhari ya bukaci magoya bayansa da su yi hakuri da yi masa kamfen har sai lokacin da doka ta yarda a fara yakin neman zabe tare da shawartarsu das u cigaba da tallata aiyuka da nasarorin da gwamnatinsa ta samu.
Da duminsa: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa
Da duminsa: Shugaba Buhari ya bukaci a dakatar da yakin neman zabensa
A dokar hukumar INEC, za a kammala gudanar da zabukan fitar da ‘yan takarar shugaban kasa, gwamnoni da ‘yan majaliar tarayya ne a ranar 7 ga watan Oktoba. Jam’iyyu kan iya fara zabukan fitar da ‘yan takarar a ranar 18 ga watan Agusta, a cewar INEC.
Za fara yakin neman zaben ‘yan takarar shugaban kasa a ranar 18 ga watan Nuwamba, yayin da ‘yan majalisar tarayya; majalisar dattijai da ta wakilai, zasu fara a ranar 1 ga watan Disamba. Gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi ba zasu fara yakin neman zabensu ba sai bayan ranar 2 ga watan Disamba.
Ranar 3 ga watan Disamba hukumar INEC ta tsayar domin mika takardun ‘yan takarar shugaban kasa da majalisun tarayya, yayinda gwamnoni da ‘yan majalisar dokoki na jiha zasu mika nasu ranar 14 ga watan Disamba.

Post a Comment

0 Comments