Da duminsa: Buhari ya isa jihar Ekiti domin yiwa dan takara APC kamfen
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa Ekiti, dake kudu maso yammacin Najeriya, domin yiwa, Kayode Fayemi dan takarar APC a zaben gwamnan jihar kamfen.
Za a gudanar da zaben gwamna a jihar Ekiti ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, mai zuwa.
Bayn shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo, ministoci da shugabancin jam'iyyar APC na kasa da kuma makwabtan jihohi sun halarci taron gangamin na yau.

Buhari a jihar Ekiti domin yiwa dan takara APC kamfen

Dandazon magoya bayan APC

Sashen manyan baki a wurin taron gangamin

Buhari ya isa jihar Ekiti domin yiwa dan takara APC kamfen
A jawabinsa a wurin taron, shugaba Buhari, ya bayyana cewar 'yan adawa na bata gwamnatinsa da rikicin makiyaya da manoma. kazalika ya bukaci jama'ar jihar ta Ekiti da kada su bata kuri'ar su wajen zaben jam'iyyar PDP da bata da wata manufa ta inaganta rayuwar su.
Tuni dai PDP, jam’iyyar adawa a kasa kuma mai mulki a jihar, ta gudanar da nata taron gangamin, wanda ya samu halartar jiga-jigan ‘ya’yanta da suka hada da tsofin gwamnoni da gwamnoni masu ci da kuma shugabanninta na kasa.
0 Comments