Online counter

Da duminsa: Buba Galadima, Shugaban R-APC ya yi hatsari

Da duminsa: Buba Galadima, Shugaban R-APC ya yi hatsari

Rahotanni dake shigowa daga kafafen yada labarai da dama sun tabbatar da cewar shugaban R-APC, Buba Galadima, ya gamu da hatsarin mota a kusa da Kano, a hanyarsa ta dawowa daga jihar Yobe inda ya je yiwa dan uwansa ta’aziyyar rasuwar diyar sa.
Galadima na tare da ‘ya’yansa biyu; Sadiq Galadima da Mohammed Galadima, da kuma wasu mutane biyu lokacin da hatsarin ya afku.
Da duminsa: Buba Galadima, Shugaban R-APC ya yi hatsari
Motar Buba Galadima da tayi hatsari
Wani jigo a tafiyar R-APC, Emmanuel Sawyerr, dake da kusanci da Buba Galadima, ya ce motar da Galadima ke ciki ta wuntsula sau da yawa yayin da hatsarin ya afku.
Sawyerr ya bayyana cewar babu asarar rai tare da sanar da cewar tuni wata motar ta debi Galadima da wadanda ke cikin motar domin garzayawa da su asibi a garin Kano domin duba lafiyarsu.
Saidai Sawyerr bai fadi abinda ya haddasa hatsarin motar ba.
Ba a san halin da Buba Galadima ke ciki ba ya zuwa yanzu.

Post a Comment

0 Comments