Online counter

Buhari ya bukaci majalisa ta tantance wasu 'yan arewa 2 a wasu manyan mukamai

Buhari ya bukaci majalisa ta tantance wasu 'yan arewa 2 a wasu manyan mukamai


- Buhari ya bukaci majalisa a basu mukami su 'yan arewa 2 a wasu manyan mukamai
- Sanata Ali zai zama wakilin arewa maso yamma a hukumar yayinda Sagir zai zama wakilin arewa ta tsakiya
- Shugaba Buhari ya bayyana cewar nadin mutanen biyu biyayya ce ga sashe na 154(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya
A yau ne majalisar dattijai ta tabbatar da samun wata takarda daga shugaban kasa Muhammadu Buhari dake bukatar su tabbatar da nadin Sanata Abba Ali daga jihar Katsina da Mohammed Sagir a matsayin mambobin a hukumar kula da bangaren shari'a.
Buhari ya bukaci majalisa ta tantance wasu 'yan arewa 2 a wasu manyan mukamai
Buhari
Sanata Ali zai zama wakilin arewa maso yamma a hukumar yayinda Sagir zai zama wakilin arewa ta tsakiya.
Shugaba Buhari ya bayyana cewar nadin mutanen biyu biyayya ce ga sashe na 154(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya.
A jawabin mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, ya mika wannan bukata ta shugaba Buhari ga kwamitin da ya dace domin daukan matakan tabbatar da su.
A yau ne shugaba Buhari ya dawo daga kasar Hollanda bayan shafe kwanaki uku a wata ziyarar aiki da ya kai.

Post a Comment

0 Comments