Online counter

Batanci ga Annabi: Jami’an tsaro sun mamaye makarantar da dalibin ya yi batancin ke karatu

Batanci ga Annabi: Jami’an tsaro sun mamaye makarantar da dalibin ya yi batancin ke karatu

Rundunar jami’an sojin Najeriya, jami’an hukumar ‘yan sanda da kuma na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun mamaye makarantar horon dalibai masu karatun zama lauya dake Legas bayan rahoton batanci da wani dalibi ya yi ga annabi Muhammad ya fara yawo a dandalin sada zumunta da kafafen yada labara.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta wallafa wani rahoto a kan wani dalibi, Madu Vitrus, da ya aika wani mummunan sako na batanci ne ga Annabin Musulunci, Annabi Muhammad, ta kafar sadarwar zamani na Whatsapp.
Yanzu haka ana kishin-kishin din wasu Musulmai masu kaushin ra’yin addini sun shirya ganin bayan wannan ‘Dalibi idan har Hukuma ba ta dauki matakin da ya dace ba.
Batanci ga Annabi: Jami’an tsaro sun mamaye makarantar da dalibin ya yi batancin ke karatu
Makarantar da dalibin ya yi batancin ke karatu
Wani ‘Dalibin Makarantar, da bai yarda a ambaci sunansa ba, ya bayyanawa Jaridar Daily Nigerian din cewa ba za su amince da irin wannan wulakanci da ake yi wa fiyayyen halitta a Musulunci ba.
Kungiyar ‘Dalibai Musulmai ta Makarantar ta koyon aikin shari’a sun nemi Hukumar makarantar ta hukunta masu zagin Annabi Muhammad SAW. Wasu dai yanzu sun yi dako su na jiran su hallaka wannan ‘Dalibi da zarar sun yi ido-hudu.
Shugaban makarantar horon lauyoyin ta jihar Legas, Tijjani Nasiru, y ace ba zai iya yin Magana a kan lamarin ba lokacin da aka tuntube shi jiya da daddare.

Post a Comment

0 Comments