Online counter

Barazanar kisa ko dauri ko kuma kamawa akan zaben 2019 duk mun shirya - inji Secondus

Barazanar kisa ko dauri ko kuma kamawa akan zaben 2019 duk mun shirya - inji Secondus

- PDP ta shirya tsaf don tunkarar zaben 2019
- A wannan karon sun ce babu abinda zai ba su tsaro koda kuwa za'a kashe su
Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus ya bayyana cewa jam’iyyun adawa basa tsoron kamawa ko dauri balle tsarewa game da zaben 2019 har ma zasu iya sadaukar da rayukansu.
Barazanar kisa ko dauri ko kuma kamawa akan zaben 2019 duk mun shirya - inji Secondus
Barazanar kisa ko dauri ko kuma kamawa akan zaben 2019 duk mun shirya - inji Secondus
Shugaban PDP ya ce a lokacin da gamayyar jam’iyyun 39 suka hadu a jiya Litinin a Abuja domin rattaba hannu kan yarjejeniyar tsayar da dan takarar shugaban kasa guda a zaben 2019 da yake gabatowa.
Ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta na tsorata duk wani dan adawa, amma ta kwana da sanin babu yadda za’ai ta murkushe ‘yan adawa baki daya (a dimukuradiyya).
Sanna ya kuma ga baiken gwamnatin APC na yunkurin kama ‘yan jam’iyyar adawar ta PDP musamman wadanda ake jiyo amonsu kafin zaben 2019 hanyar tsare su ko kulle su a gidan yari.
Ya bayyana cewa “Ko a satin da ya gabata, gwamnatin danniya ta APC ta bullo da wata doka mai kama da ta lokacin mulkin soja ta Decree 2.
Mun san dalilin da yasa suka bullo da wannan dokar gab da zaben 2019, don sun san cewa mutane duk sun juya musu baya amma kuma sun nace sai sun koma kan mulki ko ta halin kaka”.
“Amma kuma su kwana da sanin cewa ba za’a tsorata mu ba, don da magabatanmu sun tsorata lokacin da akai musu irin wannan tinziri da ba mu tarar da dimukuradiyya a yau ba. Don haka ya zama tilas mu zage damtse don tabbatar da gaskiya tayi halinta komai wahala”.
Sacondus ya kara da cewa “Jajircewa da rashin tsoro na magabatanmu ce ta sanya suka kwato kasar nan daga hannun ‘yan mulkin danniya".

Post a Comment

0 Comments