Online counter

Atiku: Majalisar dokokin Adamawa ta maida martani ga rahoton cewa yan majalisan APC na sauya sheka zuwa PDP

Atiku: Majalisar dokokin Adamawa ta maida martani ga rahoton cewa yan majalisan APC na sauya sheka zuwa PDP

Majalisar dokokin jihar Adamawa, a ranar Litinin ta ce bata da labari kan zargin sauya shekar wasu yan majalisa daga APC, zuwa PDP.
Shugaban kwamitin bayanai na majalisar, Alhaji Abubakar Isa (APC- Sheleng) ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da manema labarai a Yola.
Isa na maida martani ne ga ikirarin da jam’iyyar PDP babin jihar tayi a ranar Asabar cewa yan majalisa uku da kwamishinoni takwas masu ci sun sauya sheka zuwa jam’iyyar.
Atiku: Majalisar dokokin Adamawa ta maida martani ga rahoton cewa yan majalisan APC na sauya sheka zuwa PDP
Atiku: Majalisar dokokin Adamawa ta maida martani ga rahoton cewa yan majalisan APC na sauya sheka zuwa PDP
Yace zuwa yanzu mamba guda dake wakiltan mazabar Lamurde karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), Misis Justina Nkom ce kadai ta sanar da majalisa sauya shekarta zuwa PDP.
Haka zalika da ake Magana da kamfanin dillancin labarai, kan lamarin, kwamishinan bayanai na jihar, Malam Ahmad Sajoh yace shi mutun guda yasan yayi murabus kwamishinan kasuwanci, Alhaji Umar Daware daga majalisar zartarwa na jihar.

Post a Comment

0 Comments