Online counter

An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC Updated: 2 hours ago Author: Naziru Dalha Taura Views: 4282 Category: Labarai, Siyasa FACEBOOK EMAIL WHATSAPP FACEBOOK MESSENGER TELEGRAM - An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC - Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC - Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin Mambobin majalisar wakilai ta kasa 'yan jam'iyyar APC sun yi boren yayin zaman majalisa na yau, Laraba, saboda ambaton tsagin R-APC a zauren majalisar. Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin. An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC Zauren majalisa wakilai Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar, Mista Bode Ayorinde, ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC. Amma, wani mamba a majalisar, Mohammed Bago, ya katse masa hanzari ta hanyar shaida masa cewar majalisar ba ta da masaniyar wata jam'iyya mai suna R-APC. DUBA WANNAN: Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya Da yawan 'ya'yan jam'iyyar APC a zauren majalisar sun goyi da bayan Bago tare da hana Ayorinde cigaba da magana. Ana tsaka da wannan hargowa da yamutsi ne Dogara ya saka baki tare da kwantar da hayaniyar da ta barke.

An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC

- An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC
- Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC
- Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin
Mambobin majalisar wakilai ta kasa 'yan jam'iyyar APC sun yi boren yayin zaman majalisa na yau, Laraba, saboda ambaton tsagin R-APC a zauren majalisar.
Saidai kafin boren ya yi nisa, kakakin majalisar, Yakubu Dogara, ya shawo kan lamarin.
An samu barkewar hargowa da yamutsi a zauren majalisa saboda ambaton R-APC
Zauren majalisa wakilai
Yamutsin ya fara ne bayan mamba a majalisar, Mista Bode Ayorinde, ya gabatar da kansa a matsayin me alfahari da jam'iyyarsa ta R-APC.
Amma, wani mamba a majalisar, Mohammed Bago, ya katse masa hanzari ta hanyar shaida masa cewar majalisar ba ta da masaniyar wata jam'iyya mai suna R-APC.
Da yawan 'ya'yan jam'iyyar APC a zauren majalisar sun goyi da bayan Bago tare da hana Ayorinde cigaba da magana.
Ana tsaka da wannan hargowa da yamutsi ne Dogara ya saka baki tare da kwantar da hayaniyar da ta barke.

Post a Comment

0 Comments