Online counter

Abun kunya: An kama matashi da budurwarsa tare da iyayensa da laifin fashi a wani gida

Abun kunya: An kama matashi da budurwarsa tare da iyayensa da laifin fashi a wani gida

‘Yan sanda a ihar Legas sun kama wani matashi mai shekaru 18, Tega Teddy, da mahaifansa, Uroye Teddy, Margaret Teddy da kuma budurwarsa da laifin aikata fashi a wani gida yayin da masu gidan basa nan.
A wani jawabi da hukumar ‘yan sanda ta bakin kakakinta na jihar ta Legas, Chike Oti, ta fitar ta bayyana cewar wadanda ta kama din sun balle tare da tsallaka gidan wata mata, Folashade Odunuga, dake lamba 8 a kan titin Ade Onitiri a rukunin gidajen Harmony a unguwar Langbasa lokacin da tayi wata tafiya ta tsawon wata 3.
Budurwar Tega dake zaune kusa da gidan matar ne ta sanar da saurayinta da iyayensa batun gidan tare da shaida masu cewar mai gidan bata nan.
Abun kunya: An kama matashi da budurwarsa tare da iyayensa da laifin fashi a wani gida
Edgal Imohimi
Wata yarinyar gidan Folashade ce ta fara gano cewar an shiga gidan an yi sata, kuma ba tare da wani bata lokaci ta garzaya ta sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Da jami’an ‘yan sanda ke masa tambayoyi, Tega, ya bayyana cewar ya shiga gidan Folashade ta rufin silin ta inda yake jidar kaya yana kaiwa gidan mahaifinsa. Ya kara da cewar mahaifyarsa na taimaka masa wajen boye wasu kayan a wani kango, yayin da budurwarsa ke boye masa wasu a gidansu.
Da jami’an ‘yan sanda suka ziyarci gidan barayin, sun samu motar Folashade kirar Chevrolet wacce matashin ya ce tare da mahaifinsa suka dauko ta.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Edgal Imohimi, ya bukaci jama’a das u dauki batun kare dukiyoyinsu da muhimmanci.

Post a Comment

0 Comments