Online counter

2019: Wata mace ta sake kaddamar da takarar shugabancin kasa a Najeriya


Wata mace mai suna Mrs Eunice Atuejide, ta kaddamar ta da bukatar ta na tsayawa takarar shugabancin kasa a zaben 2019 a karkashin jam'iyyar National Interest Party, a yayin da take jawabi ga magoya bayan a jiya a Abuja, tace Najeriya ta gaza cigaba ne saboda 'son kai na wasu tsiraru'
Atuejide, wacce yar asalin jihar Enugu ne, tace kasar na bukatar shugabani wanda za su mayar da hankali wajen kawo cigaba a kasar da abinda kasar ta mallaka ba tare da nuna banbanci tsakanin mutane ba.
2019: Wata mace ta sake kaddamar da takarar shugabancin kasa a Najeriya
2019: Wata mace ta sake kaddamar da takarar shugabancin kasa a Najeriya
'Yar takarar mai shekaru 39 a duniya ta kuma bayyana cewa ba rashin ilimi, tsare-tsare ko shugabanci ne matsalar Najeriya ba, tace kawai shugabanin da muke dashi a yanzu galibu suna mayar da hankalinsu kan wasu mutane tsiraru ne.
shugaban rikon kwarya na jam'iyyar, Azeez Oladapo yace jam'iyyarsu ta mayar da hankali ne wajen zakulo matasa masu shekaru 21 zuwa 45 don basu damar rike madafan iko a kasar saboda samun cigaba a kasar.
A baya 24blog.com ta rahoto muku wata mace da ta bayyan ra'ayinta na fitowa takarar shugabancin kasar mai suna Princess Oyenike Oyedele a karkashin jam'iyyar PDP.
Oyenike Oyedele ta kaddamar da bukatar ta na fitowa takarar shugabancin kasar ne a bainar magoya bayanta a birnin New York dake Amurka.
Ta kuma yi alkawarin gwamnatinta ba za ta lamunce da cin hanci da rashawa ba inda har 'yan Najeriya suka zabe ta.

Post a Comment

0 Comments