Online counter

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana sharudda 17 ga dukkan mai son tikitin takarar shugaban kasar

Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana sharudda 17 ga dukkan mai son tikitin takarar shugaban kasar 

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta fitar da wani daftari mai feji akalla 40 dake kunshe da wasu sharuddan da ta ce dole ne duk mai neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a inuwar ta sai ya cika su.
Kunshe a cikin daftarin haka zalika jam'iyyar ta kuma bayyana cewa fom din yin takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar za ta saida shi ne akan kudi Naira miliyan 12 ga dukkan mai so.
Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana sharudda 17 ga dukkan mai son tikitin takarar shugaban kasar ta
Zaben 2019: Jam'iyyar PDP ta zayyana sharudda 17 ga dukkan mai son tikitin takarar shugaban kasar ta
24blog.ng.com dai ta samu cewa cewa mata masu sha'awar yin takara a karkashin jam'iyyar za su biya Naira miliyan 2 ne kacal.
Mun samu haka zalika cewa daftarin sharuddodin na dauke ne da sa hannun shugaban jam'iyyar na kasa Cif Prince Uche Secondus da kuma Sakataren jam'iyyar, Ummaru Tsauri.
Baya ga sharrudan sama, wasu daga cikin sharuddodin da suka dauki hankali sune na cewa dole ne sai dukkan mai neman takarar ya kasance dan jam'iyyar kuma yana taimakon ta da kudi.

Post a Comment

0 Comments