Online counter

An ci zarafin Yara 500 a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu - Jakadiyar UN

An ci zarafin Yara 500 a Sansanan Gudun Hijira cikin watannin hudu - Jakadiyar UN

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana mun samu rahoton cewa, akwai kimanin adadin yara 500 da aka ketawa haddi a sansanan gudun hijira cikin watanni hudu da suka shude.
Jakadiyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ms Comfort Lamptey, ita ta bayyana hakan a ranar Alhamis din da ta gabata da cewar akwai yara 500 da aka ci zarafin su cikin sansanan gudun hijira dake fadin kasar nan tsakanin watan Janairu da Afrilu.
Take cewa ana keta haddin yaran ne cikin kowace rana a sansanan na 'yan gudun hijira.
Lamptey tayi wannan karin haske ne yayin bikin tunawa da ranar Yaran Afirka da hukumar kare hakkin dan Adam ta Najeriya ta gudanar a babban birnin kasar nan na Abuja.
Jakadiyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ms Comfort Lamptey
Jakadiyar Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ms Comfort Lamptey
24blog.com.ng ta fahimci cewa, hukumar ta NHRC (National Human Rights Commission) ta gudanar da wannan bikin taro mai taken "kada a bar kowane yaro a baya domin ci gaban nahiyyar Afirka"
Jakadiyar ta Najeriya ta bayyana bukatar gwamnatin ta kara kaimi wajen tabbatar da bayar da kariya ga hakkin yara a kasar nan.
Take cewa, akwai tsare-tsare da dama da za a bujoro da su domin wayar da kai da kuma kira ga al'umma dangane da kare hakkin yara da kuma rage auren wuri da ake yiwa yara a kasar nan.
A nasa bangaren, Babban Sakataren hukumar NHRC, Tony Ojukwu, ya nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya gaggauta rattaba hannu kan sabuwar doka ta kare hakkin yara a kasar nan.
Ya ce, wa'adin shugaban kasa ya zama wajibi ne don kare hakkin yara da nakasa, yara da aka yi hijira da waÉ—anda aka yi wa masu cin zarafin yau da kullum.
Yake cewa akwai bukatar amincewar shugaban kasa akan wannan doka domin bayar da kariya ga hakkin yara da ake ciwa zarafi da keta ma su haddi a kowace rana.
Ya kuma roki gwamnatin jihohi akan su karbi wannan doka hannu biyu-biyu domin dabbaka ta cikin dokoki na jihohin su.

Post a Comment

0 Comments