Za a iya cewa babu wasu jarumai fitattu da suka
samu daukaka a fagen fim din Hausa kamar Ali
Nuhu da Adam A Zango, sai dai rashin jituwar da
mutanen biyu ke yi ta sa ana nuna shakku kan
wayewarsu da fargaba kan makomar masana'antar,
wacce ke fama da karancin shugabanci nagari.
Ba dai yanzu ne jaruman biyu suka fara samun
sabani ba, kuma duk da cewa an yi kokarin sulhun
tasu a baya, amma batun na ci gaba da ruruwa.

A 'yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta
musamman Instagram sun cika da kalaman batanci
da habaici, a wasu lokutan ma har da zage-zage da
ke kaiwa da komowa tsakanin magoya bayan
jaruman biyu.
Duk da cewa duka Ali Nuhu da Adam Zango ba su
fito fili sun tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin
ba, a zahiri ta ke cewa sun san abubuwan da ke
gudana, domin abin ya kai matakin da ba zai yi wu
na ce ba su sani ba.
Me ya hada fadan, kuma su waye ke ruruta shi?
Zai yi wuya ka fito ka ce ga abinda ya haddasa
wannan rashin jituwar ta baya-bayan nan, amma dai
abin da ya fito fili shi ne, akwai wasu da za a iya
dora alhakin tabarbarewar lamarin a kansu.
Ba wasu ba ne illa 'yan fada ko kuma masu dabi'ar
fadanci. Suna yawo nan da can suna fadar karya da
gaskiya domin neman gindin zama a wurin jaruman
biyu.
A don haka ya kamata a fallasa masu ruru wutar
rikin nan, a kunyata su, sannan a hukunta su idan
ba su daina ba. Wasunsu fa ba za su taba son a
zauna lafiya ba, ba za su taba son su ga an yi
sulhu ba, domin kuwa ba su da kwarewar da za su
iya fitowa a babban fim ba, in ba tare da fadanci
da banbadanci ba.
Dole ne a kauda dabi'ar nan ta fadanci ga wanda ya
kawo jarumi Kannywood, da kuma kokarin kushe
abokin hamayyarsa. Hakan na nuna irin raunin
harkar fina-finan na Hausa, domin kuwa tana nuna
cewa gaba daya masu harkar tunani daya kawai su
ke yi, kuma manufarsu ma iri daya ce.
Abu ne mai kyau ka girmama duk wanda ya daura
ka a wata hanya, ko ya taimake ka, amma za ka iya
hakan ba tare da ka ci mutuncin wasu ba.
Tasirin Ali Nuhu da A Zango a Kannywood
Yanayin zamantakewa a rayuwa da kuma lura da
abubuwan da kan faru yau da kullum sun nuna
cewa, kishi wata dabi'a ce ta mutane da dabbobi.
Zai yi wuya a ce wasu da suka yi tarayya a wani
abu guda ba sa kishi da juna.
Kishin ya kan yi tsanani idan wani ya yi wa
sa'anninsa zarra, hakan zai iya sa wasu su fara yi
masa hassada da tunanin mai ya sa wane zai fi ni.
A wasu lokutan ko da mutanen biyu suna zaune
lafiya, na kusa da su sai sun kunna wuta
tsakaninsu.
A Kannywood, sama da shekara 10 ake dangantaka
tsakanin taurari biyu Ali Nuhu da takwaransa Adam
A. Zango. Ali Nuhu ya fi Adam Zango shekaru
kuma ya riga shi fara fim.
Ko a kwanakin baya, Ali Nuhu ya shaida wa BBC
cewa shi ne ya fara saka Adam Zango a fim.
Duk da cewa akwai wasu kwararrun jaruman masu
basira, amma dai har yau ba bu kamar wadannan
biyun wajen daukaka. Haka rayuwa ta ke.
A yanzu duka jarumai masu tasowa na kokarin bin
sawun Ali da Adam, to sai dai abin takaici shi ne
matasan biyu sun dau dogon lokaci ba sa ga-
maciji.
A duniya, ba ka raba taurari da janyowa kansu
magana. Hakan na taimaka musu wajen daukar
hankulan kafofin watsa labarai. Kuma yawan
ambaton jarumi shi ya ke maida shi shahararre.
A bisa tsarin rayuwa, a kan samu sabani duk
lokacin da mutane suka yi mu'amala, ko aiki, ko
zama tare. Don haka taurari da dama suna hamayya
da juna.
Rayuwar Ali Nuhu a takaice
An haife shi a watan Maris na 1974
Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin
Kano
Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar
kasa a jihar Oyo a 1999
Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da
Turanci
Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara
fitowa a fina-fina Nollywood
Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen
Najeriya
Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa
ake masa lakabi da Sarki
Illar da fadan ka iya jawowa Kannywood
Matsalolin da Kannywood ta ke fama da su sun isa
haka. Na san cewa wasu za su ce ko a
masana'antar fina-finan India ta Bollywood da ta
Amurka Hollywood ana samun irin wannan matsala
tsakanin manyan taurari.
Haka ne, domin misali kullum ana kasayya tsakanin
Amir Khan, Salamn Khan da Sharukh Khan tun
shekarun 1990, haka kuma taurari mata da dama
suna rigima da dama kan samari, da fitowa a fim,
da kyautuka.
To sai dai karan masana'antarsu ta kai tsaiko don
haka irin wadannan matsalolin ba za su shafe ta ba.
Masana'antar Kannywood wata karamar
masana'anta ce da tun kafuwarta sama da shekara
20, take fama da suka daga mutanen da ke ganin
tana gurbata al'adun Hausa da addinin Musulunci.
Bisa la'akari da wannan, a iya cewa duk wata
badakala, da gaba, da rashin hadin kai babu abin
da za su haifarwa Kannywood din sai koma-baya.
Sama da shekara 10, har yanzu ana sanya misali da
ci gaba da tattaunawa kan hoton bidiyon tsiraici na
Maryam Hiyana. Ko irin wannan kadai ya isa a ce
ya janyo hadin kai da taka-tsantsan a masana'antar.
A yanzu rashin-jituwa tsakanin Ali Nuhu da Adam
Zango kadai ta isa ta gasganta zargin masu cewa
su kan masu harkar fina-finan ba su da tarbiyyar da
sanin ya kamata da har za su iya koyar da wata
kyakkyawar tarbiyya ko fadakar da masu kallonsu,
kamar yadda kullum suke ikirari.
Ta fuskar zamantakewa da sanin ya kamata, abin
kunya ne yadda mabiyan taurarin biyu suke musayar
mugayen kalamai, da habaici, wasu lokutan ma har
da zage-zage.
Ba makawa, wannan na nuni da irin dabi'a da
tarbiyyar masu fina-finan na Hausa tun daga kan
mutanen biyu.
Saboda dimbin magoya bayan da suke da shi,
rikicin ya kusa raba kan masana'antar ta Kannywood
gida biyu. Hakan ta sa har a kan samu wasu taurari
suna sauya sheka daga wannan bangare zuwa
wanda suka ga za su fi samun biyan bukata.
Kazalika hakan ya sa a wasu lokutan a ke kin saka
wasu taurari a fim saboda ana ganinsu a matsayin
'yan gidan abokan gaba.
Kuma shi ya sa a wasu lokutan a kan sa wadanda
ba su dace ba su taka wata rawa a wasu fina-finan,
wanda kuma hakan koma-baya ne.
Rayuwar Adam A Zano a takaice
An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar
Kaduna
Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da
aka yi
Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi
karatun Firamare
Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan
lokacin
Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher -
mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake
rawa
Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani
kamfanin kade-kade da raye-raye
Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce
shi ya shirya shi da kansa
Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara
16
'Ko a gidan giya akwai babba'
Yawan magoya baya da makiya da suke da shi ya
kuma sa duk abinda suka yi yana jawowa
Kannywood din bakin jini ko akasin haka.
Akwai ma wasu karin wasu illolin da rikicin ya ke yi
wa Kannywood. Ba manufatace in ce wane ne da
laifi ko wane ne da gaskiya ba.
Amma dai ana cewa ko a ginda giya akwai babba.
Don haka ya kamata Adam Zango ya ja kunnen
magoya bayansa da suke ganin dai-dai ne cin
mutuncin Ali Nuhu.
Shi ma a nasa bangaren, ya kamata Ali Nuhu ya
gane cewa sun jima tare da Adam Zango suna
abota da ya kamata ma a ce sun zama 'yan uwa.
Don haka shi ma ya kamata ya magantu ya gargadi
magoya bayansa.
Dole ne duka su biyun su gargadi magoya bayansu
cewa duk wanda ya kara zagin wani to sun raba-
gari.
'Babu shugabanci nagari'
Kungiyar masu fina-finai da manyan cikinsu ya
kamata su ma su tsara kansu, su zama suna
damuwa da abinda ke faruwa a Kannywood, su
samarwa kansu kima da za su iya jan kunnen duk
wanda yake kokarin raba kan 'ya'yan masana'antar.
Abin takaici ne ganin yadda ba a je ko ina ba, aka
koma ruwa bayan sulhun da darakta Falalu Dorayi
ya shirya, kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta
Kano Isma'ila Na'abba Afakallah ya jagoranta.
Mai yuwa hakan ba zai rasa nasaba da rashin
fayyace hukunci kan duk wanda aka samu da laifin
saba ka'idojin sulhun ba.
Don haka dole ne kowa ya shigo a samu domin
daidata manyan taurarin. Domin kuwa masana'antar
ta fi kowa daga cikin su biyun muhimmanci, don
haka ya kamata a tsawatar musu.