Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin
Zabe a jihar Ekiti, Jakadun Zabe
sun yi arangama

Da sanadin shafin jaridar Premium Times
mun samu rahoton cewa, mummunan rikici
ya barke da yayi sanadiyar dakatar da
gudanar da zaben tantance dan takarar
gwamna na jam'iyyar APC a jihar Ekiti.
Rahotanni dai sun bayyana cewa, da
yawan wakilai sun kada kuri'un su yayin
da wasu daga cikin wakilan jam'iyyar
suka fara gunaguni akan Ministan
Ma'adanan kasa, Kayode Fayemi, inda
suke zargin sa da sabawa ka'idoji na
gudanar da zaben.
Yanzu-Yanzu: Rikici ya barke yayin Zabe a jihar
Ekiti, Jakadun Zabe sun yi arangama
Wakilan sun yi zargin cewa, akwai
alamun tuggu da wakilan Ministan ke
kullawa yayin gudanar da zaben saboda
haka ba za samu lamunta ba inda suka
bude wuta a kan dakatar da kada kuri
Cikin gaggawa wakilan suka dakatar da
zaben yayin da wannan lamari ya sanya
jami'an tsaro suka harba harsashai bisa
saman iska domin kowa ya shiga taitayin
sa da kuma manufar kare akwatunan
zabe.
Kokarin shugaban kwamitin gudanar da
zaben, Gwamna Tanko Al-Makura na
jihar Nasarawa, na kwantar da wannan
tarzoma bai wani tasiri har zuwa karfe
5.00 na yammacin yau.