Wata rigimamiyar mata ta kaiwa
alkali farmaki a kotu yayin da ake
zaman shari'a

Hukumar Yan sandan jihar Legas ta
gurfanar da wata mace mai suna Alexia
Thomas gaban wata kotun majisatre da ke
Igbosere inda ake zarginta da kaiwa wani
babban alkali farmaki.
Rahotanni sun bayyana cewa matar ta
haddasa tashin hankali a harabar kotun
yayin da alkali ke sauraon shari'a kamar
yadda jaridar Punch ta ruwaito.
An gano cewa babban alkalin da ya
bukaci a sakaya sunansa ya aike wa
matar sammaci amma ta ki amsawa inda
ta ce ita bata san shi ba saboda haka ba
za ta amsa kirar da kotun ke yi mata ba.
Wata rigimamiyar mata ta kaiwa alkali farmaki a
kotu yayin da ake zaman shari'a
Majiyar 24blog.com.ng ta gano cewa rikicin ya
balle ne tsakanin Thomas da dan sanda
mai shigar da kara wanda ya yi yunkurin
kama ta saboda an bayar da belinta
amma bata dawo ba.

A bayar da rahoton cewa an gurfanar da
ita a gaban kotu ne a shekarar 2017 bisa
wasu laifuka uku amma bayan an bayar
da belinta sai ta ki dawowa domin a
cigaba da sauraron shari'ar ta.
Dan sandan ya yi ta neman ta amma bai
same ta sai kwatsam ya hadu da ita a
harabar kotun a ranar 17 ga watan Mayu
inda ya nemi kama ta amma tayi ta masa
kururuwa wanda hakan ya kawo cikas ga
shari'ar da akeyi a kotun.
Hakan yasa Alkalin kotun ya umurci a
gabatar da ita gaban kotun amma ta ki
amsawa inda da ce ba abinda ya dameshi
da ita sai dai alkalin ya saka an damke ta
inda aka gurfanar da ita bisa laifin tayar
da zaune tsaye.
A cewar dan sanda mai shigar da kara,
Saja Friday Mammeh, laifukan da ake
tuhumar matar dashi sun sabawa sashi
na 104(1) (a) da kuma 168(d) na dokar
masu aikata laifuka na Jihar Legas ta
shekarar 2015.
Sai dai har ila yau matar da musanta
aikata laifin da ake tuhumar ta dashi
kuma an bayar da belinta kan kudi
N250,000 tare da mutum daya da ya tsaya
mata. An dage cigaba da sauraron karar
zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2018.