Wasu Mata da za a yi gumurzu da
su a zaben 2109

A yayin da zaben shekarar 219 ke kara
matsowa, 'yan takarar kujeru daban-daban
na kara fitowa domin nuna sha'awar su ta
yin takara a jam'iyyun kasar nan.
Duk da korafin da mata keyi na ba basu
dama a siyasance kamar yadda ya
kamata, wasu mata sun bugi kirji sun fito
domin a dama da su.
1. Dakta Salma Kolo
Tsohuwar kwamishiniyar lafiya a jihar
Borno ta fito domin karawa da Sanata Ali
Ndume a takarar kujerar Sanatan jihar
Borno ta kudu a karkashin jam'iyyar APC.
2. Binta Binta: Tsohuwar kwamishiyar
mata a jihar Gombe ta bayyana niyyar ta
na tsayawa takarar kujerar majalisar
wakilai a mazabun Kaltungo!Shongom a
karkashin jam'iyyar PDP.
Wasu Mata da za a yi gumurzu da su a zaben
2109
3. Mimi Adzafe-Orubibi: Shugabar
hukumar tattara haraji ta jihar Benuwe
na son tsayawa takarar kujerar Sanata
wacce yanzu tsohon shugaban jam'iyyar
PDP, Barnabas Gemade, ke kai.
4. Sanata Bamisola Saraki: Har yanzu tana
sha'awar tsayawa takarar gwamnan jihar
Kwara duk da ta sha kaye a takarar
kujerar a 215.
Bamisola, kanwa ce wurin shugaban
majalisar dattijai, Abubakar Bukola
Saraki, kuma yanzu ta dawo jam'iyyar
APC.

5. Sanata Rose Oko: Sanata mai wakiltar
jihar Kuros Riba ta Arewa ta bayyana
niyyar ta na sake tsayawa takara a zabe
mai zuwa duk da yawan masu son maye
gurbin ta.
6. Fasto Margaret Inusa: Duk da bata yi
fice a tsakanin 'yan siyasar Najeriya ba,
Margaret zata tsaya takarar gwamna a
jam'iyyar ADP tunda gwamnan jihar,
Simon Lalong, zai kara tsayawa takara a
jam'iyyar APC.
7. Aisha Dahiru Ahmed: Tsohuwar
mamba a majalisar wakilai daga jihar
Yola karkashin jam'iyyar PDP da yanzu ta
koma APC inda take burin yin takarar
kujerar Sanatan jihar Adamawa ta
tsakiya, kujerar da ta fadi zaben ta a
shekarar 215 a karkashin jam'iyyar PDP.