Wani Barawo ya mika kansa ga
Yansanda bayan buhun gyadan da
ya sata ya makalkale masa a wuya
(Hotuna)

Wani lamari mai ban dariya, man ban
haushi, kuma mai ban tausayi ya faru da
wani matashi da ya shahara wajen aikata
sata, musamman yake bi cikin dare yana
farautar kayan mutane, sai dai Hausawa
na cewa idan ana cin kasa, a kiyayi na
shuri.
Wannan matashin mai halin bera mai
suna Frank Buhet ya takalo abinda yafi
karfinsa, inda yaje ya sace ma wata
tsohuwa buhun gyada da tsakar dare,
amma koda yayi kokarin sauke buhun
daga kansa a lokacin da ya isa gida, sai
abu yaci tura, yayi yayi amma ina, buhu
ya makale masa a wuya.

Barawo
Wannan lamari mai ban al’ajabi ya faru
ne a kasar Tanzania, matashin bayan ya
fito daga gidan nasa ya dinga bi layi layi
yana neman agaji a sauke masa gyadar
amma an kasa, kai har kwanciya yayi a
kasa ko buhun zai fado, amma abu yaci
tura.
https://www.youtube.com/watch?v=RAzjv2l_vQw
NAIJ.com ta ruwaito bayan Buhet ya
fahimci ya debo ruwan dafa kansa da
wannan buhun da ya sato ne sai ya
garzaya ofishin Yansanda, inda ya mika
kansa da kansa, kuma ya bayyana musu
yadda lamarin ya wakana.
Sai dai fa hatta a Ofishin Yansandan,
buhun nan yaki sauka, kuma duk kokarin
a Yansanda suka yi na kwantalo buhun
daga kansa amma lamarin ya gagari
kundila, don haka ne ya bayyana ma
Yansandan gidan da yayi satar, kuma ya
rokesu sun emo masa Tsohuwar don
kada nauyi ya kashe shi.
Barawon