Turkiyya: Turawa mahaukata ne da
suke kira ayi wa Al-Qurani
kwaskwarima

- Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya Ibrahim
Kalın ya bayyana cewa, daga nan har zuwa
tashin alkiyama za aci gaba da tsare
Alkur'ani Mai Tsarki.
- Turkiyya ta mayar da martani ga wasu 'yan
siyasa marubuta su 300.
Turkiyya: Turawa mahaukata ne da suke kira ayi wa
Al-Qurani kwaskwarima
Kakakin Shugaban Kasar Turkiyya
Ibrahim Kalın ya bayyana cewa, daga nan
har zuwa tashin alkiyama za aci gaba da
tsare Alkur'ani Mai Tsarki.
Turkiyya ta mayar da martani ga wasu
'yan siyasa marubuta su 300.

Mutanen sun hada da tsohon shugaban
kasar Faransa Nicolas Sarkozy wadanda
suka nemi da a yi wa Alkur'ani Mai tsarki
gyare-gyare saboda sunce yana dauke da
bayanan nuna kyama ga Yahudu da
Nasara.
Kakakin na Shugaban kasar Turkiyya
Ibrahim Kalın yace,
"Alkur'ani Mai Tsarki ba allon kowa da
kowa ba ne na rubuta goge ba. Littafinmu
ne Mai tsarki. Kuma daga nan har zuwa
tashin Alkiyama za a ci gaba da tsare Shi.
Kyamar Yahudawa wani tsarine da ya fito
daga Turai. Kasashen Yamma da ke son
magance wannan matsala to su tambayi
Kasashensu. Wannan na nuna wauta da
jahilci a zamanin yau."
Shi ma Ministan Harkokin Wajen
Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya mayar da
martani ga 'yan siyasar na Faransa da
cewa, "Wannan kalami nasu alama ce ta
nuna kyama ga Musulunci. Sun wuce gona
da iri. Idan aka yi irin wadannan kalamai
me ya ke faru wa a Turai? Sai akai hare-
hare kan Masallatan Juma'a."
Yace, a tsawon tarihi Kasashen Yamma
sun zalunci Yahudawa. "Kun zalunci
Yahudawa, Daular Usmaniyya da
Jamhuriyar Turkiyya. Musulmai ne suka
tsare su."
Cavusoğlu ya ci gaba da cewa, babu
kyamar Yahudawa a wajen Musulmi.
Hakan ya samawa imaninmu da
Alkur'aninmu Mai Girma. Shin wa za ku
ba wa darasi.