Turawa sun bukaci a gaggauta cire
ayoyin dake sukar Yahudu da
Nasara daga Al-Qurani

- Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba
da tofin Allah tsine kan da'awar da tsohon
shugaban Faransa,Nicolas Sarkozy da wasu
gungun mutane 300 suke yi na a gaggauta
share duk wasu ayoyin da ke sukar
Yahudawa da Kiristoci daga Al Kur'ani mai
tsarki.
Turawa sun bukaci a gaggauta cire ayoyin dake
sukar Yahudu da Nasara daga Al-Qurani
Jiga-jigan gwamnatin Turkiyya na ci gaba
da tofin Allah tsine kan da'awar da
tsohon shugaban Faransa,Nicolas Sarkozy
da wasu gungun mutane 300 suke yi na a
gaggauta share duk wasu ayoyin da ke
sukar Yahudawa da Kiristoci daga Al
Kur'ani mai tsarki.
A jerin mutanen da ke sahun gaban
wajen yin wannan farfagandar
akwai,tsohon shugaban kasar
Faransa,Nicolas Sarkozy,Philippe Val,
tsohon shugaban jaridar "Charlie Hebdo"
wacce daman ta yi kaurin suna wajen yin
zanen batanci kan mafificin
halitta,Manzon Allah Muhammad tsira da
amincin Allah su tabbata a gare
shi,tsohon magajin garin birnin
Paris,Bertrand Delanoe,tsaffin ministoci
3,jiga-jigan addinai daban-daban,
masana,taurarun fina-finai,masu aikin
hannu da dai sauran su.

Masu bakar da'awar suka ce,
"A gaggauta share duk wasu ayoyin da ke
kiran Musulmai da su kyamaci ko kuma
su yaki Yahudawa da Kiristoci.Saboda
barin su, babbar barazana ce ga rayuwar
mabiya wadannan addinan".
Kamar a sauran sassan duniya, samun
wannan labarin ke da wuya,shugabannin
kasar Turkiyya suka yi tofin Allah tsine
da kuma tsawatawa Farasansawan.
A shafinsa na Twitter,mai magana da
yawun shugaban kasar Turkiyya,Ibrahim
Kalin ya ce,
"Al Kur'ani,littafi ne mai tsarki.Allah zai
ci gaba da tsare shi har karshen duniya.Al
Kur'ani ba allo ba ne da za a dinka rubutu
kansa,kana a dinka goge shi a duk
lokacin da aka ga dama.Littafinmu ne
mai tsarki.Kyamar Yahudawa akida ce da
ta bulla a tsakiyar Turai.Turawan da ke
bukatar warware bakin zaren wannan
matsalar, sun waiwayi baya don bincikar
tarihinsu.Babu wani jahilci da ya kai
wannan bukatar tasu,a wannan duniyar
tamu ta yau,inda ake tinkaho da
wayewa".
Mataimakin shugaban gwamnatin
Turkiyya,Bekir Bozdağ ma ya wallafa
albarkacin bakinsa a Twitter inda ya ce,
"Daya daga cikin manya-manyan makiyan
Islama,tsohon shugaban Faransa da wasu
gungun Faransawa 300 sun shafa wa
Islama bakin fenti ta hanyar bayyana
bukatarsu ta a gaggauta cire "Ayoyin da
ke kiran jama'a da su kyamaci Yahudawa
da Kiristoci" daga Kur'ani.Wadannan su
ne shashashu,sakarkaru,marasa
tunani,gidadawa,dangin Abu Jahil, kana
'yan DAESH a Yamma.Ba Sarkozy ba,ko
da illahirin makiya Islama za su hade
mana kai,ba zasu taba kawo daidai da
aya daya tilo ko kuma sauya wani abu
daga cikin Kur'ani, har sai an busa kaho".
Ministan harkokin wajen
Turkiyya,Mevlüt Çavuşoğlu kuma cewa
ya yi,
"Wannan wata alama ce da ke nuna irin
yadda kyama da nuna wariya ga
Musulmai suka kamari a Turai.Tuni
wadannan mutane suka wuce gona da iri.
Shin me kuke tsammanin zai afku, bayan
da suka furta irin wadannan kalaman ?
Za a dinka kai wa masallatai hare-hare a
Turai.A tsawon tarihinku kun ci gaba da
zaluntar Yahudawa.Musulmai ne suka
cece su ta hanyar karbar bakwancinsu
hannaye biyu a tsawon karnoni da dama,
musamman ma a zamanin daular
Musulunci ta Usmaniyya,inda aka kare
martabarsu tare da karrama su.Bamu san
me ake nufi da kyamar Yahudu ba.Don
babu irin wannan akidar a addini da
kuma littafinmu.Yayin da a yau, a Turai
nuna wariyar launin fata,kyamar masu
neman mafaka da 'yan gudun hijira da
kuma waninsa, ke ci gaba da samun
gindin zama.Jam'iyyun siyasa masu
wariyar launin fata na cin karansu babu
babbaka a kasashenku.In dai da gaske
kuke,ku fara yakar su mana.Shin wanne
ne 'yancin da kuke ambato? Shin wa zaku
bai wa darasi? ".
Ministan yawon bude ido da raya al'adu
na Turkiyya,Numan Kurtulmuş ma, ya
nuna bacin ransa inda ya ce,
"Wannan batun da suka zo da shi ba
komai ba ne face, gidadanci da kuma
wauta.Allah wadai ga wadanda ke sukar
mabiya wannan tsarkaken littafin
"Kur'ani" da kuma wannan babban
addinin mai suna salama "Islam".Ina
fatan al'umar kasashen Turai zasu yi
kunnen uwar shegu da wadannan
maganganun na badala da rashin
hankali".