Tarihi: Ladi Kwali, mace ta daya
tilo dake jikin takardar kudin
Najeriya

'Yan Najeriya da dama basu san labarin
matar da aka sanya hoton ta a bayan naira
20 da suke kashewa yau da kullum ba. Matar
da hoton ta ke bayan naira 20 na kudin
Najeriya wata fitaciyar mai sana'ar kera
tukwane ce mai suna Ladi Kwali.
An haifi Ladi Kwali ne a wani kauye mai
suna Kwali, wanda ke yankin Gwari da a
yanzu yake karkashin birnin tarayya
Abuja, dama dai sana'ar kera tukwane
shahareren sana'a ne ga matan yankin.
Kwali ta taso ne a gidansu inda mata
sana'ar kirar tukwane don su sami abin
da zasu tallafawa kansu kuma itama ta
koya sana'ar wajen kanwar mahaifiyarta
tun tana karamar yarinya.
A cewar kanin ta mai suna Mallam
Mekaniki Kyebese: "Tun lokacin da take
karama, tana da matukar hazaka wajen
kirar tukwane da wasu abubuwan, galibi
ma mutane kan saye tukwanenta tun
kafin ta kai kasuwa.
Da taimakon wani dan kasar Ingila mai
sha'awar daukan hotunan tukwane,
Michael Cardew, Kwali tayi suna a
duniya a shekarun 1950s. Daga baya an
nada Cardew a matsayin jami'i mai kula
da kera tukwane a ma'aikatan kasuwanci
da masana'antu a shekarar 1951 inda ya
kafa makarantar koyar da kera tukwane
na Abuja a tare da Kwali a 1952 inda
suka kwashe shekaru 15 suna koyar da
kera tukwane.
Takaitacen tarihin Ladi Dosei Kwali, mace ta farko
da aka saka hoton ta a kudin Najeriya
Takaitacen tarihin Ladi Dosei Kwali, mace
Takaitacen tarihin Ladi Dosei Kwali, mace ta farko
da aka saka hoton ta a kudin Najeriya
Takaitacen tarihin Ladi Dosei Kwali, mace ta farko
da aka saka hoton ta a kudin Najeriya
Tukwanen da Kwali ke karewa sunyi
suna saboda kyawun su da inganci hakan
yasa Sarkin Abuja a wannan lokacin,
Suleiman Barau ya saya tukwane da yawa
daga wurinta don kayata fadar sa.
Daga bisan Kwali da Cardew sun tafi
ziyara a kasar Amurka da Landan inda
aka gabatar da ayyukan ta wurare da
dama kuma mutane na ta sha'awa da
mamakin irin baiwar da take dashi.
Takaitacen tarihin Ladi Dosei Kwali, mace ta farko
da aka saka hoton ta a kudin Najeriya
Ga wasu daga cikin lambobin yaba da
karamawa da ta samu:
1) A shekarar 1962 an karrama ta da MBE
(Member of the Order of the British
Empire), a kuma 1977 jami'ar Ahmadu
Bello da ke Zaria ta karrama ta da digirin
girmamawa na Dacta, (Honorary
Doctorate).
2) Gwamnatin Najeriya ta karramata da
lambar yabo mafi girma a Najeriya na
ilimi wato 'Nigerian National Order of
Merit Award'
3) A shekarar 1981, ta samu lambar yabo
na (OON) wato Officer of the Order if the
Niger.
4) A sanya sunanta a wani layi a babban
birnin tarayya Abuja wato Ladi Kwali
Street.
5) An canja sunan makarantar koyar da
kera tukwanen na Abuja zuwa Ladi
Kwali Pottery.
6) An sanya hoton ta a bayan naira 20 na
kudin Najeriya, itace mace na farko da
aka sanya hoton ta a kudin Najeriya.
Bayan Cardew ya rasu a shekarar 1983,
Ladi Kwali ta rasu a ranar 12 ga watan
Augusta tana da shekaru 59 a duniya a
garin Minna.