Shugaba Buhari ya sauka a garin
Daura domin halartar taron
jam'iyyar APC a mazabar sa

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun
samu rahoton cewa, shugaban kasa
Muhammadu Buhari ya sauka a mahaifar sa
ta garin Daura dake jihar Katsina domin
halartar taron jam'iyyar APC na mazabar sa
a gobe Asabar 5 ga watan Mayu.
Kamfanin dillancin labarai na najeriya ya
ruwaito cewa, shugaba Buhari ya isa
mahaifar ta sa ne da misalin karfe 5.30
na yammacin ranar Juma'a ta yau.
Shugaba Buhari ya sauka a garin Daura domin
halartar taron jam'iyyar APC a mazabar sa

NAIJ.com ta fahimci cewa, shugaba Buhari
zai halarci taron jam'iyyar sa ta APC a
mazabar sa ta Sarkin Yara dake garin
Daura kamar yadda za a gudanar da
wannan taro na jam'iyyar a kowace
mazaba dake fadin kasar nan.

Shugaban mazabar Sarkin Yara, Mallam
Ali Mani ya bayyana cewa tuni an
kammala shirye-shirye domin samun
nasarar gudanar da wannan taro tare da
gargadin mambobin jam'iyyar akan
kiyaye doka.