Shirye-shirye sun yi nisa domin sake shirya fim
din Mujadala, wanda aka fara yi shekara 18 da ta
gabata, kamar yadda kamfanin da ke shirya fim
din ya bayyana.

Kamfanin Mai Shadda Investment ya ce za a fara
nadar shirin a ranar 10 ga watan Mayu.
Jarumi Umar M Shareef shi ne zai maye gurbin
marigayi Ahmad S. Nuhu, wanda shi ne ya fito a
matsayin jarumi a fim din na asali.
Fim din Mujadala ya shahara sosai a tsakanin
ma'abota fina-finan Hausa.
Fitaccen jarumi kuma mai shirya fim Ali Nuhu,
wanda dan uwa ne ga Ahmad S. Nuhu, shi ne zai
tsara fim din da kuma bada umarni.
Marigayi Ahmad S. Nuhu ya mutu ne a farkon
shekara ta 2007 bayan wani mummunan hadarin
mota da ya yi a hanyar Azare zuwa Maiduguri.
Mutuwarsa ta tayar da hankalin masu ruwa da tsaki
a Kannywood da kuma magoya baya.
Ya kasance jarumi mai tashe da farin jini, wanda
kuma aka ce abokan aikinsa na jin dadin hulda da
shi.
Kamfanin Mai Shadda ya wallafa a shafinsa na
Instagram cewa Mujadala shiri ne wanda har yanzu
'yan kallo "suna daukin gani bayan shekara kusan
18 da fitowarsa".