Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan
sanda sai yayi jamb

- Duk masu shirin neman aikin 'Dan sanda
sai sun zage damtse a wannan karon,
sakamakon sabbin tsare-tsaren da aka fito
da su
- Kuma Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa
ya umarci da'a saka ido wajen gani an dauki
wadanda suka cancanta ba tare da alfarma
ba
Babban Sufeton 'Yan sanda na kasa IGP
Ibrahim K. Idris NPM, mni, ya bayyana
cewa, sabbin jami'an da za'a dauka dole
sai sun rubuta jarrabawar tantancewa ta
JAMB kafin daukar tasu. Ya bayyana
hakan ne ta bakin kakakin rundunar kasa
ACP, Jimoh Moshood.
Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a
dauka ya rubuta JAMB
A cewar rundunar, wannan wani yunkuri
ne na tabbatar da sahihanci da kuma
tsantseni wajen daukar duk wadanda
suke son zama jami'an 'Yan sandan da
za'a fara daga gobe 7 ga watan Mayu.
Babban Sufeton IGP Ibrahim K. Idris, ya
kuma gargadi dukkannin jami'an
rundunar na jahohi 36 tare da birnin
tarayya Abuja da su kasance sun bi
dokokin da aka sanya wajen tantance
wadanda za'a dauka aikin na 'Dan sanda.
Ibrahim K. Idris yayin da yake jawabi ga
manyan jami'an 'Yan sanda ta hannun
mataimakinsa DIG Emmanuel Inyang,
yayi kira gare su da su tabbatar da cewa
an bi doka wajen fara tantancewar a
gobe Litinin. Sannan ya kuma gargade su
da su cire son kai yayin tantancewar.

Sai dai wani sabon salo da rundunar ta
bullo da shi na batun zana jarrabawar
JAMB kafin samun shiga aikin, wanda
hakan na a matsayin karon farko da ta
faru a runduna.
Bayan tantancewar lafiyar jiki yanzu
masu neman aikin zasu gudanar da
jarrabawar rubutu da JAMB zata shirya
domin tabbatar da an dauki wadanda
suka cancanta.
Sannan kuma za'a gwada lafiyar
kowannensu, da tantance karfin gani
daga nesa da na kusa da bambance
launin kaloli da kuma gwajin karfin jin
kunne da gwajin ciwon tarin fuka da
ciwon siga da hawan jini da cuta mai
karya garkuwar jiki da kuma gwajin juna
biyu ga mata.
Daga nan ne kuma za'a gudanar da
tantancewar karfin zurfin tunani da
dabi'a da kuma gwajin shaye-shaye
kwayoyi.
Sabon salo: Dole ne kowanne 'Dan sanda da za'a
dauka ya rubuta JAMB
Babban Sufeton ya kuma umarci
mataimakin nasa da ya tabbatar da cewa
sun sanya idanu a yayin tantancewar don
tababtar da an gudanar da ita yadda ya
kamata a duk fadin jahohin Najeriya da
kuma Abuja.
Haka zalika, an shawarci iyaye da masu
neman aikin na 'Dan sanda da su kai
korafinsu yayin da suka ga wani abu na
dai-dai ba ga lambobin wayar da suka
bayar.
08076036011, 08037036257, 08034360919,
08037855951, 08065823054, 08036753589.
A sanarwar da kakakin rundunar ACP,
Jimoh Moshood ya sanyawa hannu.f