Rikicin Masarautar Saudiyya:
Yarima Fahad yayi kira akan yiwa
Sarki Salman juyin mulki

Wani sabon rahoto da sanadin shafin jaridar
TRT Hausa ya bayyana cewa, yariman kasar
Saudiyya, Khalid Bin Farhan, ya na neman
hadin kai wajen kwace mulkin kasar daga
hannun Sarkin Salman.
Yariman yayi ikirarin cewa, a halin yanzu
kaso 99 cikin 100 na ahalin masarautar
sun shirya tsaf domin karbe karagar
mulki daga hannun Sarki Salman da
iyalan sa.
Jaridar ta ruwaito cewa, Yariman wanda
ya fake a kasar Jamus tun a shekarar
2013, ya nemi wasu 'yan uwan sa masu
jinin sarauta akan su hada kai domin
yiwa Sarki Salman Bin Abdulaziz Al Saud.
24blog.com.ng ta fahimci cewa, Yarima Farhan
wanda a halin yanzu yake kasar Jamus a
matsayin dan gudun hijira ya yi kira ga
Yarima Ahmad bin Abdulaziz da kuma
dan uwan sa Yarima Muqrin Bin
Abdulaziz akan su zamto tsintsiya
madauri daya wajen hadawa Sarki
Salman kayan sa a hannu.
Rikicin Masarautar Saudiyya: Yarima Fahad yayi
kira akan yiwa Sarki Salman juyin mulki
A yayin ganawa da manema labarai na
jaridar Middle East Khalid, ya bayyana
cewa mulki Sarki Salman ba bu abinda ya
haifar face babbar asara ga masarautar ta
Saudiyya da kuma duniyar Musulunci
baki daya.

A kalaman sa, "Idan Ahmad da Muqrin
suka zama tsintsinya madauri daya, ina
da tabbacin cewa kaso 99 cikina 100 na
ahalin masarautar Saudiyya, jami'an
tsaro da dakarun soji zasu goya musu
baya domin sun yi mani alkawarin
hakan"
"Ina son na yi amfani da wannan dama
domin kiran Kawunnai na Ahmad da
Muqrin, 'ya'yan Marigayi Sarki Abdullah
bin Abdul-Aziz wanda har ya kwanta
dama yana yiwa Addinin Islam hidima,
domin dawo da wannan martaba."
Ya kara da cewa, "Kasar Saudiyya dutse
ce mai cike makil da wuta wanda ke gaf
da yin kwaranya."