Rahotanni daga karamar hukumar Birnin Gwari na
Jihar Kaduna sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe
akalla mutane 45 a kauyen Gwaska da ke yankin.

Lamarin dai ya faru ne kasa da mako guda bayan
wani hari da wasu 'yan bindiga suka kai a garin
Janruwa inda suka kashe wasu masu aikin hakar
ma'adinai da dama.
'Yan bindigan wadanda ake kyautata zaton sun fito
ne daga wasu dazuzzuka na jihar Zamfara sun kone
kusan daukacin gidajen da ke kauyen Gwaska da
kuma kauyen Kuiga.
Wani dan asalin yankin Zubairu Abdurrauf, Dan
masanin Birnin Gwari ya shaida wa BBC cewa
akasarin wadanda aka kashe 'yan sakai ne da ke
kokarin kare garuruwansu daga hare haren 'yan
bindigan da suka addabi al'umma.
A lokacin da ya ziyarci yankin a 'yan kwanakin nan,
babban Sufeton 'yan sandan Najeriya Ibrahim Idris
ya yi alkawarin tura karin 'yan sanda yankin na Birnin
Gwari.
A 'yan shekarun nan dai ana samun tashin hankali
da kashe-kashen jama'a a jihar Kaduna da ma
wadansu jihohi makwabta.