Raddi: Shirya nike da binciken da
Buhari yace zai yi a kaina -
Obasanjo

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo,
ya mayar da martani da shugaba
Muhammadu Buhari akan zargin
almubazzarancin $16 billion kan samar da
wutan lantarki.
A wani jawabin ya mai magana da yawun
Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya saki, ya
ce shugaba Muhammadu Buhari yayi
magana a kan jahilci.
Yayinda ya karbi bakuncin magoya
bayansa a fadar shugaban kasa a yau
Talata, shugaba Buhari yace tsohon
shugaban kasa ya amsa tambayoyi a kan
kudaden.
Raddi: Shirya nike da binciken da Buhari yace zai
yi a kaina - Obasanjo
Amma a raddinsa, tsohon shugaba
Obasanjo yace: "Amsan abu ne mai sauki;
wutan lantarkin na cikin ayyukan
bunkasa wutan lantarki 7 da kuma
na'urorin gas 18..."
Ya bukaci shugaba Buhari ya karanta
littafinsa mai suna 'My Watch' wanda ya
wallafa saboda duk yayi wadannan
bayanai a ciki.

Yace idan kuma Buhari bai iya karatu ba,
ya umurci hadimansa da su tayashi
karantawa da kuma yi masa bayanin da
zai fahimta.