Mayun karnuka sun cinye yara
shida, sun saka jama'a cikin firgici

Wasu mayun karnuka da suka kwace suka
bazama cikin wasu kauyuka sun hallaka yara
shida a Arewacin kasar Indiya.
'Yan sanda sun ce jama'a sun shiga cikin
halin dimuwa sakamakon wannan
annoba. Mazauna kauyukan na cigaba da
tsare yaran su a gida sannan suna jin
tsoron fita gonakin su.
Jami'in 'yan sanda, Anand Kulkarni, ya
shaidawa majiyar mu ta wayar tarho
cewar yara shida ne karnukan suka kashe
a yankin Sitafur dake Uttar Pradesh.
Karnukan sun kashe yaran dake tsakanin
shekaru biyar zuwa 12 cikin kwanaki
goma.
Mayun karnuka sun cinye yara shida, sun saka
jama'a cikin firgici
"Karnukan, bakwai zuwa tara, na yawo
ne suna neman kananan yara.
Daga watan Nuwamba zuwa yanzu sun
kashe a kalla yara 12," a cewar Kulkarni.

Karnukan na kai farmaki kan yara a
wuraren da babu jama'a musamman
gidajen gona ko yayin da yara suka fita
bayan gari domin kiwo ko bahaya.
Duk da samun asarar rai sakamakon
harin karnuka ba bakon abu bane a kasar
Indiya, saidai wannan shine mafi muni
da ya taba faruwa a yanki guda.