Majalisar dattijai na bincikar yadda
biliyoyin kudaden fanshon sojoji
suka bace ba

- Ana cin zalin kananan kuratan sojoji a
NAjetiya
- Su kuma sojin su ke yaki a dazuka, sun
kuma fi mutuwa a filin daga
- Manyan soji ke wawure fanshonsu su boye
domin kudin ruwa
Majalisar dattijai na bincikar yadda biliyoyin
kudaden fanshon sojoji suka bace bat
Binciken majalisar Dattijai na wawure
kudaden kananan sojoji na fansho ya
nuna cewa akalla N44b ne a tsakanin
shekarun 2013-2017 basu isa ga masu
hakki ba inda aka canja akalar kudaden
zuwa wasu asusun don neman riba.
A bayanan na baya-bayan nan, Ministar
Kudi Adeosun, tace an kuma gano wasu
biliyan kusan biyu a wani assusun suna
bacci babu mai-su a wani babban bankin
'yan kasuwa, bayan da aka tattaro
kudaden aka kaisu asusun bai-daya na
TSA

Asusun na ansho, ya amshi N13.5 billion
a 2015, N16.6 billion a 2016 da N15. 422
billion a 2017, inji ofishin Akanta Janar
na kasa nan.
Kwamitin ya baiwa hukumar zuwa talata
da su fitar masa da dukkan takardu da
bayanai da ake bukata don aga inda
kudaden suka makale, ko kuma wa ya
handame su.