Ma'aurata sun tona wa kansu asiri
gaban kotu a jihar Oyo, leka kuji

- Wasu ma'aurata da ke zaune a garin
Ibadan sun yiwa junansu tonon silili a gaban
Alkali
- Mijin ya roki kotu ta raba aurensu saboda
tsabar sata da yace matar nasa ke yi masa
- Matar nasa tace ita ba barauniya bane
amma ta kwashe wasu kayansa ta sayar ne
saboda ya dena kula da ita
Wata kotu da ke zamanta a Mapo da ke
Ibadan a jihar Oyo ta raba auren wani
Akeem Folorunsho da Fatima saboda sata
da yayi ikirarin matar na yi masa.
Ma'auratan dai sun shafe shekaru biyu
suna tare kuma Allah ya albarci auren da
'da daya.
Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN)
ta ruwaito cewa Alkalin kotun Cif
Ademola Odunade ya amince da bukatar
Akeem inda ya raba auren.
Ma'aurata sun tona wa kansu asiri gaban kotu a
jihar Oyo, leka kuji
Akeem ya shaidawa kotu cewa matar
nasa tana son ganin bayansa ne da
halinta na sata. "Duk lokain da na fita
daga gida don neman abinci, Fatima tana
caje aljihun tufafi na kuma ta sace min
kudi.
"Bayan abinci da kayan jaririn mu da na
samar a gidan, ina bata N2,000 duk
mako." inji shi.
Akeem kuma ya kara da cewa bayan ta
bar gidansa, ta sake dawowa gidan inda
ta balle kofan gidan kuma ta dauke masa
kayayakin gida da suka hada da firinji,
katifa, DVD player, kayan jin waka da
sauransu.
A bangarenta, Fatima, wadda malaman
makaranta ce ta musanta zargin daya ke
mata na sata, ta fadawa kotun cewa mijin
nata ya dena kulawa da ita ne duk da
cewa bata gama murmurewa daga tiyata
da akayi mata ba. Hakan yasa ta dauke
wasu kayayakinsa ta sayar don ta biya wa
kanta bukatu.