Kwarankwatsa ta fado a jihar
Taraba, ta kashe mutane biyar tare
da raunata Fasto

A kalla mutane biyar ne suka mutu yayin da
wasu da yawa suka samu raunuka bayan
fadowar kwarankwatsa a Jalingo, babban
birnin jihar Taraba.
Kwarankwatsar ta lalata gidaje, wurin
bauta, ofisoshi, makarantu, da sauran su.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar
Taraba, ASP David Misal, ya tabbatar d
da faruwar lamarin ga manema labarai.
"Tabbas an samu fadowar tsawa mai
karfin gaske (kwarankwatsa) da tayi
sanadiyar mutuwar mutane hudu bayan
da tsawar ta haddasa faduwar karfen
sabis a kansu.
Kwarankwatsa ta fado a jihar Taraba, ta kashe
mutane biyar tare da raunata Fasto
Ya kara da cewar mai yiwuwa adadin
mutanen da abin ya shafa ya karu.
Shugaban kungiyar likitoci a jihar Taraba,
Dakta Dashe Dasogot, ya tabbatar wa da
jaridar Daily Trust cewar an kawo gawar
mutane biyar asibitin kwararru na
Jalingo bayan fadowar kwarankwatsar.
Dasogot ya nunawa manema labarai
wasu bishiyoyi da gine-gine a cikin
asibitin da faduwar karfen ta shafa.
Wata shaidar gani da ido, Uwargida
Henrietta Anthony, ta bayyana cewar uku
daga cikin 'yan uwan ta, Aisha Useni,
Felicia Istifanus da Istiah James, na daga
cikin mutane hudun da suka mutu.
Kazalika fadowar tsawar ta shafi wani
ginin Coci tare da jikkata wasu mutane
bakwai da wani Fasto, Ravaran John
Jerome, dake cikin ta lokacin da ta rushe.