Kwanan nan zamu garkame
shugaban PDP Secondus da
abokan badakalar sa - Fadar
shugaban kasa

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewar nan
bada dadewa ba zata garkame shugaban
jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, tare
da ragowar mutanen da suka wawure
makudan kudade lokacin mulkin Jonathan.
Fadar shugaban kasar na wadannan
kalamai ne a matsayin martani ga wata
wasika da jam'iyyar PDP ta aikewa
majalisar dinkin duniya tana mai zargin
Buhari da almundahana daban-daban.
Mataimakin shugaban kasa na
musamman a bangaren yada labarai,
Mallam Garba Shehu, a wata sanarwa da
ya fitar, yau, Litinin, ya zargi jam'iyyar
PDP da yin siyasa da gaba tare da neman
dawowa gwamnati ta kowacce hanya.
Shugaban jam'iyyar PDP; Uche Secondus
Garba Shehu ya bayyana cewar,
Secondus, da duk ragowar 'ya'yan
jam'iyyar PDP da suka wawure makudan
kudade lokacin mulkin jam'iyyar su, zasu
gurfana gaban shari'a domin girbar
abinda suka shuka.

Kazalika, ya ce kokarin jam'iyyar PDP na
yaudarar majalisar dinkin duniya ba zai
samu karbuwa saboda kimar da Buhari
keda ita a idon duniya.
Jam'iyyar PDP ta aike da wata wasika
zuwa ga ofishin babban sakataren
majalisar dinkin duniya tana mai
bayyana cewar shugaba Buhari na goyon
bayan makiyayan dake kashe mutane a
Najeriya.