Kwamitin majalisar Dattijai ya zargi
ministar kudi da barnatar da
dukiyar jama'a

- An gano makudan kudade a bankuna a
boye bayan bude asusun bai daya na TSA
- A lokacin jin bahasi a majalisa, kwamitin
ya zargi ministar da barna
- Kudaden N540m, sun hada da kudaden ta
kashe su ga aikin kwangila
Kwamitin majalisar Dattijai ya zargi ministar kudi
da barnatar da dukiyar jama'a
Wani kwamiti da majalisar dattijai ta
kafa kan bincikar kudaden da ake ta
cetowa daga adanannnun kudaden
gwamnati, ya gano cewa ita ma ministar
ta dan yi almubazziranci da kudade da
suka kai rabin biliyan.
N540m ta kashe a wani kamfani, kan
kwangilar binciko mata kudaden
gwamnati da suka buya, aiki da, a cewar
kwamitin, na ofishin Akanta Janar na
kasa ne.