Kungiyar musulmi ta JNI ta bukaci
jama'a su farga saboda jami'an
tsaro sunyi sanyi

- Kungiyar Jama'atu Nasrul Islam JNI tayi
wani kira ga yan Najeriya a ranar Alhamis
- Kungiyar ta bukaci al'umma su farga kuma
su sanya ido batun tsaro saboda yadda hare-
hare da kara tsananta
- Kungiyar tayi ikirarin cewa hukumomin
tsaro sunyi sakwa-sakwa ne shiyasa yan
ta'adan suka sake yunkuro wa
A jiya Alhamis ne kungiyar addinin
musulunci na Jama'atu Nasrul Islam JNI
tayi kira ka yan Nageriya dasu farga
saboda su kare kansu daga makiyansu da
ke hare-hare a kan 'yan Nageriya.
Wannan kiran ya fito ne daga bakin
Khalid Abubakar, Sakatare Janar na JNI a
wani taro daya gudana a Kaduna akan
bam din daya tashi a Mubi wanda ya yi
sanadiyyar mutuwar mutane 85 da
jikkata wasu da dama.
Kungiyar Jama'atu ta mika wani muhimmin sako
ga yan Najeriya
Kungiyar ta ce ya kamata a kawo karshen
kashe-kashen da akeyi a jihohin Borno,
Kaduna, Nassarawa, Benue da Zamfara.