Kasar Canada na son rage yawan
'yan Najeriya da ke tururuwa zuwa
kasarta

- 'Yan Najeriya na yawan guduwa kasashe
masu arziki domin rayuwa
- A yanzu kasar Kanada ke kwasar jama'a
daga Indiya, Larai da Afirka
- Kasar tana so ta rage yawan 'yan Najeriya
masu tururuwa zuwa kasar ta
Kasar Canada na son rage yawan 'yan Najeriya da
ke tururuwa zuwa kasarta
Ofishin jakadancin kasar Kanada dake
nan Abuja, ya mika korafinsa ga
hukumoomi a Najeriya, dama hadin kan
takwarorinsa na Amurka, kan yadda 'yan
kasar nan na Najeriya ke tururuwa zuwa
cikin kasarsa babu kakkautawa.
A bincikensu, sun gano cewa, matasa a
Najeriya, na karbar bisar Amurka da
niyyar ziyara kawai domin shakatawa,
amma sai su wullar da paspon nasu da
sun isa Amurka, su je iyakar kasar ta
Canada, su fada cikin kasar ba bisa ka'ida
ba, kuma suyi zamansu su ki dawowa.

A kokarin 'yan Najeriya dai, na guje wa
bakin talauci na kasarsu, sukan tsere
kasashen waje, inda sukan ada mugun
hannu, ko a bautar dasu, ko sahara ko
teku su hadiye su, ko kuma su isa amma
a dawo dasu.
A bayan hawan shugaban Amurka, sai
suka daina zuwa Amurkar da niyyar
zaman gudun hijira, saboda rantsuwar
sabon shugaba Trump na koro masu
zuwa ba bisa ka'ida ba, ina suka koma
bibiyar kasashe masu makwabtaka da
Amurkar.