Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari
ga iyalan Shehu Isyaku Rabi'u da
Kanawa

- Shugaba Buhari ya rubuto kasida ta rashin
babban malami da aka yi a Kano
- Ya taba kama dattijon a mulkinsa na soja a
1985
- Isiyaka Rabiu dattijon kirki ne da ya rayu a
Kano
Karanta ta'aziyyar shugaba Buhari ga iyalan Shehu
Isyaku Rabi'u da Kanawa
Shugaba Muhammadu Buhari, ta bakin
kakakinsa, Femi Adesina, ya aiko
ta'aziyyarsa ga maluman Kano, da ma
jama'arta, kan rasuwar Alhaji Isyaka
Rabiu, hamshakin dan-kasuwa da ya rasu
a daren jiya.
A sanarwar, shugaban yayi alhinin rashin
babban malamin, inda ya kira shi da
dattijon arziki, dan kasuwa da malami,
wanda kowa zaiyi rashi, a fadin kasar
nan.

'Rashin na Malam, wani babban rashi ne
ga Malumta, karatu, da ma kasuwanci,
wanda kowa ke jimami. Dattijon, ya bar
baya mai kyau, muna fatan iyalansa zasu
dora kan ayyukansa na alheri,
musamman kasuwanci da samarwa
samari ayyukan yi, muna fata Allah ya
rahamshe shi, ya yafe masa zunubbansa,
ya kuma kyautata bayansa.'
A shekarun mulkin soja dai, shugaba
Buhari ya daure Malamin bisa zargin
almundahana da boye abinci don yayi
tsada, amma an sako shi ba tare da
samun laifinsa a kotu ba. Sai dai an zargi
sojoji da cuzgunawa da ma fasa
rumbunan ajiyar abincin 'yan kasuwar
lokacin, inda aka raba wa talakawa.
Rade-radi da suka yi ta yawo kan dattijon
da cewa wai yana yanka kai, kuma wai
matsafi ne wanda wai ya saci marigayi
wazirin Kano, Sheikh Isa Waziri, duk sun
zamo sharri ne kawai ake wa malamin
saboda jahiltar kirkinsa.