ja kunnen Sifeton Yan Sanda -
Saraki da Dogara sun kai karan IGP
wajen Buhari

Shugaban majalisan dattawa, Bukola Saraki,
da kakakin majalisan wakilai, Yakubu
Dogara, sun laburatwa shugaba Muhammadu
Buhari ya wajabtawa sifeto janar na
hukumar yan sanda, Ibrahim Idris, bin
dokan kasa.
Shugabannin majalisan dokokin wadanda
sukayi jawabi ga manema labaran fadar
shugaban kasa bayan ganawarsu da
shugaba Buhari cewa sun nuna rashin
amincewarsu da yadda aka ci mutuncin
sanata mai wakiltar Kogi ta yamma, Dino
Melaye.
Ka ja kunnen Sifeton Yan Sanda - Saraki da Dogara
sun kai karan IGP wajen Buhari
Sun ce abinda sifeto janar na yan sanda
yayi na gurfanar da Dino Melaye kan
gadon asibiti jahilci ne kuma babu inda
za’a gurfanar da mutum ko da dan
baranda ne a kan gadon asibiti.
Shugabannin sun baiwa shugaba Buhari
tabbacin cewa za su shirya kasafin kudin
2018 a wannan mako.
Kamar yadda muka kawo da safiyar yau
cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi
wata ganawar gaggawa da shugaban
majalisar dattijai, Bukola Saraki, da
Kakakin majalisan wakilai, Yakubu
Dogara a yau.