Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira
ga jama'a su guji wadannan
abubuwa

- Anyi kira ga jama'a su guji kiba da maiko
- An mayar da kayan kwalam da makwalashe
abinci
- Kiwon lafiya na farawa daga ciki ne
Hukumar lafiya ta duniya ta yi kira ga jama'a su
guji wadannan abubuwa
Hukumar lafiya ta duniya, tayi kira ga
jama'a dasu guji kayan abinci masu
sanya qiba, da taiba, kamar maiqo da
zaqi, musamman ga wadanda basu
essasaye wato motsa jiki.
An sami karuwar masu mutuwa sosai
saboda sunki bin wannan shawara,
musamman cikin matasa, a kuma
kasashe masu tasowa, wadanda arziki
yayi musu gwauron kamu. Ita dai
hukumar a jiya ta fitar da sanarwar,
ganin a shekara mutum 17m ke mutuwa
daga kibar.
Abinci mai maiko kan sanya masu kin
motsa jiki zama wuri daya tara mai
watau kwalestarol a cikin jini, wanda shi
kuma yana zuwa ne ya toshe jijiyoyi ya
hana jini gudana yadda ya kamata.
Abincina masu sanya qiba sun hada da
siga, kwai, jan nama, kitse na dabba,
bota na biredi, da ma kayan abincin da
aka soya, musamman ga manya, illar tafi
yawa.
A ci kayan ganye da abinci mai saukin
siga, a ci kayan itatuwa, aci daga kayan
gona ba na kanti ba, a ci a sha a kuma
duba jini da ma motsa jiki, in ba haka ba,
likita zai sami aboki da wuri.