Hotunan zangar-zangar neman
sakin Zakzaky dake gudana a
Legas

Magoya bayan kungiyar ‘yan uwa Musulmi
da aka fi sani da “Shi’a” yanzu haka na can
garin Legas inda suke gudanar da zanga-
zangar neman sakin shugaban su, Sheikh
Ibrahim El-Zakzaky, da matar sa, Zeenah.
Gwamnatin Najeriya na cigaba da tsare
El-Zakzaky tun bayan kama shi a
shekarar 2015 sakamakon wata hatsaniya
da ta afku tsakanin magoya bayan sad a
dakarun sojin Najeriya.
Tun bayan garkame shi magoya bayan sa
ke gudanar da zanga-zangar neman a
sako shi a sassan kasar nan, musamman
jihohin arewacin Najeriya, inda keda
yawan musulmi.
Hotunan zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake
gudana a Legas
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana
a Legas
Sati biyu da suka wuce an samu
barkewar rikici tsakanin magoya bayan
Sheikh El-Zakzaky da jami’an hukumar
‘yan sanda a Abuja yayin da suke
gudanar da zanga-zanga.

Wannan shine karo na farko da magoya
bayan Shi’a ke gudanar da zanga-zanga a
wata jihar dake kudancin Najeriya.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da
manyan lauyoyi sun yi alla-wadai da
cigaba da tsare Zakzaky da gwamnatin
Najeriya ke yi, duk da cewar kotu ta
bayar da umarnin a sake shi.
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana
a Legas
Zangar-zangar neman sakin Zakzaky dake gudana
a Legas