Gwamnatin tarayya ta bayyana
haramtattun makamai, manyan
motoci da aka gano a gidan
Sambo Dasuki

Gwamnatin tarayya a yau Talata ta
bayyanawa babban kotun tarayya da ke
zaune a Abuja manyan motoci 11 da muggan
makamai da suka gano a gidan tsohon NSA,
Sambo Dasuki, a gidansa da ke Abuja a wani
farmaki da hukumar DSS ta kai a watan
Yulin 2015.
INSTALL
A bank account in 4 min?
It takes 4 min to open a savings account right
on your phone and get your account number!
Ad
Gwamnatin tarayya ta bayyanawa kotu
wadannan abubuwa ta mai bada shaida a
kotu, William Obiora, wani jami'in DSS
wanda yayi musharaka a farmakin da
hukumar ta kai tsakanin ranan 16 da 17
na watan Yuli, 2015.
Lauyan gwamnati ya bayyanawa kotu
cewa wasu daga cikin makaman
mallakan gwamnati ne amma Dasuki ya
sace yayinda ake ofis.
Gwamnatin tarayya ta bayyana haramtattun
makamai, manyan motoci da aka gano a gidan
Sambo Dasuki
Dasuki ya kasance a garkame a ofishin
hukumar DSS tun watan Disanban 2015.
Obiora, wanda ya bada shaida an boye
fuskarsa domin bashi kariya. An lissafo
abubuwa 29 da aka gano a gidansa.

Gwamnatin shugaba Buhari ta ki sakin
Kanal Sambo Dasuki duk da cewa kotuna
daban-daban sun bada belinsa. Ba da
dadewan nan ba, wata kotun ta sake
bada belinsa amma hukumar DSS ta ki
sakinsa.
24blog.com.ng ta kawo muku rahoton cewa
Kotun koli ta kasa wadda ake yi wa
lakabi da kotun Allah-ya-isa ta yanke
hukuncin karshe a game da takaddamar
shari'ar da ake ta tafkawa a tsakanin
tsohon mai ba sohon shugaban kasa
Goodluck Jonathan shawara ta fannin
tsaro, Kanal Sambo Dasuki (mai ritaya)
da ake cigaba da yi a wani boyayyen
wuri na musamman.
Da suke yanke hukuncin, kotun a ta
bakin babban alkalin kotun Mai shari'a
Ajembi Eko ya bayyana cewa kotun ta
kuma gano cewa ba hukumar EFCC ce ba
ke dauke da alhakin cigaba da tsare
Kanal Dasuki din.