Gwamnatin Saudiyya zata kashe
dala biliyan 35 ba ga mahajjata ba,
a'a, ga masu shaqatawa

- Kasashen musulmi na ganin Saudiyya a
matsayin limamiya a harkar addinin Islama
- Saudiyyar ta kawo sauye-sauye da suke
daure wa musulmin kayi, inda suke ganin
kamar dujal ne ya iso
- Ta'addanci da kungiyoyi keyi da sunan
addinin Islama ya sanya shugabannin sauya
akalar kasar su
Gwamnatin Saudiyya zata kashe dala biliyan 35 ba
ga mahajjata ba, a'a, ga masu shaqatawa
A jiya ne, masarautar Saudiyya ta
bayyana wani sabon shiri da za'a kashe
dala biiyan akalla 35, kusan Titiliyan
goma na nairori, wadda za'a kashe kan
harkar fina-finai da shakatawar samarii
da turawa masu ziyarar kasar kafin 2020.
Kudaden za'a samar dasu ne domin a
saukaka zafin ra'ayin addinin Islama a
kasar ta Saudiyya, wannan kua na nufin
wasu kasashen musulmin zasu koma
kallon kasar ta Saudiyya a matsayin kasar
badala ba ta qara imani ba.