Gwamna El-Rufai ya bayyana dan
siyasar da zai maye gurbin Shehu
Sani a majalisar dattawa

Rikicin siyasar jihar Kaduna daya kunno kai
a tsakanin gwamnan jihar, Malam Nasiru
Ahmad El-Rufai da Sanatocin jihar Kaduna,
Shehu Sani, Suleiman Hunkuyi da kuma
Sanata Danjuma Lar yayi kamari, inda ta kai
ga gwamnan na barazanar kada su zabe.
Premium Times ta ruwaito El-Rufai ya
bayyana wani hadiminsa, mashawarcinsa
akan lamurran siyasa, Uba Sani a
matsayin dan takarar da yake muradin
ganin ya kada Sanata Shehu Sani a
takarar kujerar sanatan Kaduna ta
tsakiya a zabuka 2019.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin
yakin neman zabe na shuwagabannin
kananan hukumomi da yayi a mazabar
sanatoriyar Kaduna ta tsakiya, inda ya yi
kira ga jama’a da su tabbata sun kada
Shehu Sani daga kujerarsa.
Gwamna El-Rufai da Uba Sani
Majiyar NAIJ.com ta ruwaito El-Rufai ya
mika kokon bararsa ga yayan jam’iyyar
APC, da kuma jama’an gari dasu jajirce
wajen ganin sun zabi Uba Sani a
matsayin wakilin al’ummar Kaduna ta
tsakiya a majalisar dattawa.
Wannan kira da gwamnan yayi ya biyo
bayan matakin tabbatar da takarar Uba
Sani a matsayin sanata da
shuwagabannin jam’iyyun APC na
kananan hukumomi 6 cikin gida 7 da
suka samar da Sanatoriya ta tsakiya suka
yi ne.
Daga karshe gwamnan yayi kira ga
jama’a da yan siyasa da kowa ya tabbata
ya bi Doka da Oda a zaben kananan
hukumomin jihar da zai gudana a ranar
Asabar 12 ga watan Mayu.