Gaba da gaban ta: ‘Yan fashin da
suka tare hanyar Buratai a
Adamawa sun ji maza, kalli
hotunan su

A daya daga cikin labaran naij.com na yau,
kun ji cewar wasu ‘yan fashi da suka tare
hanyar Numan zuwa Yola a jihar Adamawa
sun gamu da fushin dakarun sojin tawagar
shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Tukur
Yusuf Buratai.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun
darektan hukumar sojin, Birgediya Texas
Chukwu, ta bayyana cewar a jiya Asabar,
5 ga watan Mayu, tawagar shugaban sojin
kasa ta kama wasu ‘yan fashi da suka
tare hanya suke zaluntar mutane kuma
Buratai ya biyo hanya. ‘Yan fashin sun
tare babbar hanyar inda suke cin Karen
su ba babbaka kafin tawagar Buratai ta
zo wuce wa ta hanyar.
‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa
‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa
‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa
An kama wasu makamai a hannun ‘yan
fashin da suka hada da; bindigar baushe
guda uku, adduna, da wasu tarkacen
tsibbu.
Sanarwar ta bayyana cewar tuni dakarun
sojin suka mika ‘yan fashin hannun
jami’an ‘yan sanda domin zurfafa bincike
da gurfanar das u gaban shari’a.

Hukumar soji ta bukaci jama’a da suke
samar da bayanai masu muhimmanci ga
jami’an tsaro a kan kari domin daukan
mataki kafin lamari ya rincabe.
makaman ‘yan fashin da suka tare hanyar Buratai a
Adamawa
Makaman ‘yan fashin da suka tare hanyar Buratai a
Adamawa
‘Yan fashin da suka tare hanyar Buratai a Adamawa